Rundunar Dakarun Tsaro na ‘Civil Defence’ da ke jihar Abia, sun tabbatar da mutuwar mutane 19 sakamakon gobarar da ta tashi lokacin da bututun man gas ya kama da wuta a wasu kauyuka biyu da ke cikin Karamar Hukumar Osisioma.
Benifo Eze, wanda shi ne kwamandan dakarun ne ya bayyana wa manema labarai haka a yau Juma’a a Abuja.
Ya ce an samu mutane 16 ciki har da mace daya ta suka mutu a kauyen Umuaduru, sai kuma wasu uku da suka mutu a cikin gidajen su a kauyen Umuimo.
Ya ce gobarar ta tashi ne a kauyen Umuimo bayan da wata mata mai sana’ar abinci ta tashi wajen karfe uku na dare ta kunna wutar dora girkin ta.
Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa matar da mijin ta sun kubuta, amma gidan su ya kone kurmus.