HABAICIN ATIKU GA BUHARI: ‘Ni ba zan shafe wata shida ban nada ministoci ba’

0

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya jajjada cewa shi ba irin Shugaba Muhammadu Buhari ba ne, da zai yi likimon watanni shida kafin ya nada ministoci.

Atiku ya ce idan ‘yan Najeriya suka zabe shi, to zai zabi ministocin sa tun ma kafin a rantsar da shi a ranar 29 Ga Mayu, 2019, kuma ya tabbatar da cewa ba zai yi zaben-tumun-dare ba.

A wani takaitaccen bayani da Atiku ya yi a shafin sa na tweeter, ya ce ba zai dauki tsawon wata shida kafin ya nada ministoci ba, idan aka zabe shi ya zama shugaban kasa.

Ya ce Najeriya na bukatar shugaba wanda ke da kuzari da saurin daukar matakin da zai sake maida kasar nan a kan saiti sosai.

Masana tattallin arziki da dama sun yi ittifakin cewa watanni shida da Buhari ya dauka kafin ya nada ministoci bayan an rantsar da shi, hakan ne ya assasa kangin matsin tattalin arziki da Najeriya ta shiga shekara daya bayan hawan Buhari mulki.

Share.

game da Author