Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa an gano wani shiri da wasu ke yi domin hargitsa mata taron gangami na kasa da za ta gudanar a Fatakwal, inda za ta zabi dan takarar shugaban kasa na zaben 2019.
Ta ce babu wani kulle-kulle ko makircin da zai hana jam’iyyar gudanar da zaben fidda-gwanin da za ta yi ranar Asabar, 6 Ga Oktoba, a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.
Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar ne, Kola Ologbondiyan, ya bayyana haka ga manema labarai bayan kammala taron Kwamitin Zartaswa na Kasa na PDP, wanda ya gudana ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce gangamin zai yi matukar nasara, duk kuwa da yunkurin da wasu ke yi ta karkashin kasa da nufin kawo wa taron cikas, don kada PDP ta samu damar fitar da na ta dan takarar.
PDP za ta yi na ta gangamin ne a ranakun 6 da kuma 7 Ga Oktoba.
Olabondiyan ya ce akwai wasu masu hana idon su barci, kullum su na ta kulle-kullen yadda za su haifar da cikas ga taron da PDP za ta fara daga gobe Asabar a Fatakwal.
“Mun gayyaci kungiyoyin kasashen duniya su dauki wannan magana da muhimmanci cewa, akwai kulle-kullen da ake ta yi domin ganin an kawo wa gangamin PDP cikas, don kada su iya zaben wanda zai yi takara da Shugaba Muhammadu Buhari a 2019.
“Kuma mu na sanar da dukkanin ‘yan Najeriya wannan shiri da wasu ke kullawa.
Daga nan ya kara da cewa amma ba za su fasa gudanar da taron ba, kuma duk wasu algunguman da ke neman yi wa taron cikas, ba za su yi nasara ba.
An tambaye shi batun jami’an tsaro, sai Olabondiyan ya ce sun aika wa hukumar ‘yan sanda da INEC sanarwar yin taro, kamar yadda doka ta yi umarni a yi.