‘Batutuwan da mu ka tattauna da Oshiomhole’ – Gwamnonin APC

0

Wasu gwamnonin jam’iyyar APC su bakwai da sarkar rikicin zaben fidda-gwani ta rikirkice masu, sun garzaya domin gudanar da wani taron gaggawa tare da shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole.

An gudanar da taron a Abuja, ranar Alhamis.

Zaben fidda-gwanin gwamnoni da sanatoci na wasu jihohi ya zo da rudani da hargitsi sosai, har jirgin jam’iyyar na neman yin tangal-tangal a wasu jihohin da abin ya shafa.

Rigingimum da suka biyo baya ne suka kara tabbatar da cewa akwai matsala kwance a kasa idan ba a gaggauta warware ta ba.

KAKA-TSARA-KAKA

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC dai ta kara jaddada cewa daga ranar Lahadi, 7 Ga Satumba, ta rufe duk wani zaben-fidda gwani. Domin a ranar Litinin ne, 8 Ga Oktoba za ta karbi sunayen wadanda suka yi nasara a zabukan fidda-gwani.

Dalili kenan ma APC ta shirya gudanar da na ta taron a ranar Asabar, 6 Ga Oktoba, a Abuja, yayin da ita ma PDP ta shirya yin na ta gangamin a ranar 6 Ga Oktoba, a Fatakwal.

A wannan ranar ce za a zabi ‘yan takarar shugaban kasa, kuma daga ranar babu sauran batun wani zaben da ba na dan takarar shugaba kasa ba, tunda shi ne na karshe kamar yadda dokar INEC ta gindaya.

Gwamnonin da wannan katankatana ta shafa sun hada da: Rochas Okorocha na Imo, Abubakar Bagudu na Kebbi, Rotimi Akeredolu na Ondo, Abdul’aziz Yari na Zamfara, Simon Lalong na Filato, Tanko Almakura na Nasarawa da Ibekunle Amosun na Ogun.

GA DARA GA DARE YA YI

Bayan fitowar su daga taron ganawa da shugaban jam’iyyar Adams Oshimhole, wanda ya fara yi wa manema labarai jawabi shi ne Gwamnan jihar Zamfara, Abdul’ziz Yari, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar gwamnoni ta kasa.

Daga Yari har har sauran gwamnonin, duk tatsuniyar su guda ce; wato tsoro, shakku da fargabar abin da ke tunkarar su daga nan zuwa ranar Lahadi, da misalin karfe 12 na dare.

Sun bayyana wa manema lbarai cewa sun tattauna matasalar da ke tattare da APC idan har ba a sasanta an yi wasu zabukan fidda gwani ba daga nan zuwa ranar Lahadi da karfe 12 na dare.

Yari ya ce maganar gaskiya lokaci ya kure wa jam’iyyar APC, amma dai za su gaggauta, su hanzarta kuma su zabura cikin kankanen lokaci domin a yi zabuka a jihohin da ba a gudanar da zabukan ba.

INEC dai ta ce duk inda ba a yi zabe daga nan zuwa ranar Lahadi da karfe 12 dare ba, to jam’iyyar ba ta da dan takarar wannan kujerar da ake ja-in-ja a kan ta kenan.

Gwamnonin sun ce hankulan su a tashe ya ke, domin lokaci na karatowa, kuma ga taron gangamin jam’iyya na kasa baki daya da za a yi a Abuja, ranar Asabar.

Yawancin wadannan gwamnonin dai su na fama da tankiya ne ko dai inda aka zabi wani sanata da su shan inuwa daya, ko kuma inda gwamna ke ganin abin nan da Hausawa ke cewa ‘ruwa ya kare wa dan kada’.

A jihar Zamfara an soke zaben fidda-gwani na ‘yan takarar gwamna, wanda hakan na nuni da cewa abin bai yi wa gwamna Yari dadi ba.

Share.

game da Author