Ministan Harkokin Noma da Inganta Karkaka, Audu Ogbeh, ya ce idan ba a gaggauta daukar matakan da suka dace ba, to Najeriya za ta shiga cikin babbar matalar karancin shinkafa.
Ogbeh ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke bude bukin Hukumar Kula da Irin Kayan Noma ta Kasa da kuma Bajekolin Kayan Noma da Iri na 2018, a Abuja.
Ministan ya ce ambaliya ta shafi wasu manyan jihohin da suka shahara wajen noman shinkafa, ya na mai kara yin gargadin cewa idan ba a dauki mataki ba da hanzari, bayan daukewar ruwan damina, to za a fuskanci matsanancin karancin shinkafa a kasar nan.
“Sai mun tashi tsaye mun samo hanyar da za mu tallafa wa manoman da ambaliya ta yi wa barna; musamman a jihohi kamar Jigawa, Kebbi, Anambra, Kogi inda manoma da yawa abin ya fi shafa. Manoma sun rasa duk shinkafar da suka noma.
“Amma akwai wani irin shinkafa wanda ambaliya ba ta lahanta shi, kamar irin faro 66 da 67.
“Muna fatan zan gaba kadan za mu nemo irin wannan samfurin shinkafar mu bai wa manoman mu su rika shukawa.”
Ya kara da cewa da zarar ruwan sama ya dauke, gwamnati za ta kara wa manoma karfin guiwar sake dasa irin shinkafa, domin kasa na da saurin laima, yadda zuwa karshen watan Disamba za a iya samun irin shinkafa sosai.
Idan ba haka muka yi ba kuwa, to za mu fuskanci matsalar karancin shinkafa, gero, dawa da masara cikin shekara mai zuwa.”
Discussion about this post