Kwamitin Sake Fasalin ’Yan Sandan SARS ya fara zaman karbar korafe-korafe

0

Kwamitin Shugaban Kasa na Sake Fasalin ’Yan Sandan Farmakin Dakile Fashi Da Makami, da aka fi sani da SARS, ya fara zaman sauraren korafe-korafen jama’a.
Kwamitin wanda ya fara zaman sa a bainar jama’a, jiya Litinin 23 zuwa 25 Ga Satumba, tuni har ya karfi korafe-korafe 27.

Babban Sakataren Hukumar Kula da ’Yancin Jama’a, Tony Ojukwu ne ya bayyana haka jiya Litinin a Abuja, a lokacin da ya ke gabatar da jawabin maraba, yayin fara zaman kwamitin a bainar jama’a.

Ya ce ana sauraren korafe-korafen a sarari ne domin hukumar ta samu damar isa ga al’umma.

“Sannan kuma ana so a tabbatar da an bi komai a kan ka’ida, muhamman inda duk aka samu shaida da kuma tabbacin cewa jami’an SARS sun danne wa mutane ‘yanci ko hakkin su a lokacin da suke gudanar da aikin su.

“Ana kuma so a ji ta bakin wadanda ake zargi da kuma wanda aka tauye wa hakki domin a san irin matakin da ya yi daidai a dauka.”

Ojukwu ya ce an bai wa kwamitin nauyin bincike da kuma sauraren korafe-korafen jama’a dangane da yadda SARS ke cin zarafin jama’a a cikin shekaru biyu da suka gabata zuwa yanzu.

Mataimakin Sufurtandan ’Yan Sanda Benjamin Okolo, wanda ke wakiltar Sufeto Janar Idris Ibrahim, ya tabbatar da cewa jami’an ‘yan sanda za su bada hadin kai domin cimma nasarar da aka neman samu a aikin kwamitin.

Ya ce ba wani wanda jami’an tsaro za su ci wa zarafi, komin irin munin zargi ko shaidar da zai gabatar da ita a gaban kwamitin.

Share.

game da Author