Gwamnan jihar Barno Kashim Shettima ya bayyana cewa gwamnati za ta samar wa masu fama da cutar koda kula kyauta a asibitin da gwamnati ke ginawa a Maiduguri.
Shettima yace shugaban kamfanin Matrix Energy Abdulkabir Aliyu ya fara gina asibitin a matsayin tallafa wa masu fama da wannan cutar amma yanzu haka gwamnati ta karbi aikin don ta karisa.
Ya ce gwamnati ta saka kayan aiki masu tsada a asibitin sannan bayan an kammala asibitin masu fama da wannan cutar za su sami kula kyauta.
A karshe Shettima yace gwamnati ta dawo da manyan likitoci biyu da suka shahara a kula da masu fama da wannan cuta domin horas da ma’aikatan wannan asibitin.