RIKICIN KADUNA: Gwamnatin Kaduna ta rage tsawon lokuttan zaman gida na dole

0

A sanarwa ta musamman da gwamnatin Kaduna ta fitar da ranar Talata, ta sanar da rage awowin zaman gida na dole da gwamnati ta saka a fadin jihar.

Sai dai kuma ba janye talalar kwata-kwata aka yi ba,gwamnati ta rage lokacin ne saboda mutane su dan samu su garzaya Kasuwa su siya abinci.

A kasuwan Magani da Kajuru, dokar hana fita zai fara ne daga 5 na yamma zuwa shida na safe.

Amma kuma unguwannin Kabala West, Kabala Doki, Sabon-Tasha, Narayi da Maraban Rido, ba a basu daman yin motsi ko da nan da can ba ne. Dokar na nan kamar yadda take a da a wadannan unguwanni.

Sauran unguwannin Kaduna kuma, an basu da ga karfe 1 zuwa 5 na yammacin Talata, wanda da ga nan kuma dokar za ta ci gaba kamar da har sai an sake sanar da canji.

Gwamnati ta gargadi mutane da su tabbata sun bi wannan doka sau da kafa, cewa jami’an tsaro ba za su sausauta wa duk wanda aka kama yana karya doka ba.

Share.

game da Author