Farashin kayan masarufi ya kara yin sama – NBS

0

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta bayyana cewa farashin kayayyaki da kuma na hada-hadar ayyuka na yau da kullum ya kar yin tashin-gwauron-zabo sama, a karo na biyu a jere cikin watanni biyu.

NBS ta ce kafin watan da ya gabata, an jera watanni 18 farashin bai hauhawa sama ba.

Rahoton ya kuma tabbatar da cewa farashin kayan abinci ya tashi daga hauhawar da ya yi ya kai kashi 13.16 a cikin watan Satumba, zuwa 13.31 a cikin watan Oktoba.

Najeriya na ci gaba da kasancewa cikin halin rashin isassun kudaden gudanar da ayyukan raya kasa da ke cikin kasafin 2018.

Ko a cikin makon da ya gabata sai da PRRMIUM TIMES ta buga labarin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi Majalisar Dattawa ta amince masa kara ciwo bashin dala biliyan 2.88.

Share.

game da Author