Babbar Kotun Jihar Katsina, ta ci gaba da shari’ar tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shema, wanda ake tuhuma da salwantar naira biliyan 11 a hannun sa a tsawon shekaru takwas da ya yi ya na mulkin jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa Shema na fuskantar tuhumar ce a karkashin Mai Shari’a Ibrahim Maikaita, dangane da salwantar naira bilyan 11.
Babban Lauya mai kare Shema, Joseph Daudu, ya yi fatali da ci gaba da sauraren karar, a bisa dalilin san a cewa ai sun daukaka kara a gaban Babbar Kotun Daukaka Kara ta Kaduna, dangane da rashin yarda da wasu kwafen takardu a matsayin hujjojin mai gabatar da shaida na biyu da na uku da wani mai bayar da shaida mai suna Ibrahim Dabo ya gabatar wa kotu.
Daudu, wanda lauya Adebayo Adedaji ya wakilta, ya roki kotu ta daga zaman har zuwa ranar 26 Ga Oktoba, 2018, ranar da za su iya sanin matsayin hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta Kaduna ta yanke.
Sai dai kuma mai gabatar da kara, Babban Lauya Jibrin Okutepa, ya ki yarda da cewa a daga zaman kotun, shi kuma ya roki mai shari’a ya ba mai shaida na biyu daga bankin Keystone Bank damar shigowa kotu ya gabatar da shaidar sa.
Mai Shari’a ya yi watsi da rokon lauya mai kare Shema, nan take ya bada umarnin mai gabatar da shaida na biyu, daga Keystone Bank, Abdulmalik Iyal ya shiga ya gabatar da ta sa shaida.
Iyal Manajan Shiyya ne na Bankin Keystone.
Iyal ya bayyana inda ya gabatar da kwafen bayanan asusun ajiyar Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu ta Jihar Katsina.
Daga nan sai Mai Shari’a Maikaita ya daga kara zuwa 16 Ga Oktoba, domin ci gaba da saurare.