2019: INEC za ta raba Katin Rajistar Zabe cikin kafin karshen 2018

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyaya cewa ta na kokarin ganin ta raba wa duk wanda ya yi rajista katin san a na rajista na dindindin nan da watan Nuwamba.

Shugaban Hukumar, Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai, bayan da ya bude taron sanin makamar aiki domin tantance kudaden da ake kashewa wajen gudanar da zabubbuka a kasashen Afrika ta Yamma.

“Karin hasken da zan yi a yanzu shi ne mun rigaya mun bugo Katin Rajistar Zabe na Dindindin (PVC) na dukkan wadanda suka yi rajista a watanni uku na farkon 2018, kuma mu na kan aikin buga katin wadanda suka yi rajista a watanni uku na tsakiyar shekara kuma na wadanda suka yi rajista a watanni uku bayan tsakiyar shekara. To kun ga kenan, nan da karshen Nuwamba za a kammala buga katin rajistar na dindindin kenan.

Yakubu ya tabbatar da cewa duk wani wanda ya san ya yi rajista kuma ya nemi a sauya masa saboda canjin wuri ko garin zama zai iya shafar sa a lokacin zabe, duk za su samu na su kafin zaben 2019.

Sai dai kuma ya ce babu batun sake neman sauya wa mutum kati saboda canja gari ko jihar da ya ke, domin an dakatar da wannan tare da yin rajista har sai bayan zabe kuma.

Share.

game da Author