Buhari ya umarci Yusuf Usman ya tafi hutun dole har sai an kammala bincike a kansa

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugaban hukumar Inshorar lafiya ta Kasa Yusuf Usman da tafi hutun dole domin ba kwamitin da gwamnati ta nada daman gudanar da bincike kan harkallar da ake zargin sa da tafkawa a hukumar.

A wata shimfidaddiyar wasika da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya mika wa shugaban hukumar, Yusuf Usman, Buhari ya ce Yusuf ya tafi hutun dole daga ranar 5 ga watan Nuwamba.

Tuni har an nada kwamitin mutam 7 da za su gudanar da binciken sannan su mika wa gwamnati abin da suka bankado da shawarwari akan aikin da suka yi.

An ba kwamiti mako biyu su kammala binciken.

Share.

game da Author