Likitoci a asibitin koyarwa na jami’ar Abuja dake Gwagwalada tare da wasu likitocin da hadin kungiyar ‘Global Peace Initiatives’ sun yi nasarar raba wasu ‘yan biyu da aka haife su manne da juna.
Likitan da ya jagoranci fidar kuma jami’in kungiyar ‘Global Peace Initiatives’ Nuhu Kwajafa ya sanar da haka a shafin sa na Instagram.
Kwajafa ya kuma jinjinawa tallafin biyan kudaden fidar da kakakin majalisar dokoki na kasa Yakubu Dogara ya yi wa iyayen wadannan yara.
A karshe kakakin Dogara, Hassan Turaki ya bayyana wa manema labarai cewa Dogara ya tallafa wa iyayen wadannan yara ne baya ya saurari kukan su da aka sanar dashi inda nan take ya ce a kai su asibiti ayi musu aiki.