Mutane 81,481 na dauke da cutar Kanjamau a jihar Ondo

0

Shugaban hukumar hana yaduwar cutar Kanjamau ta kasa (NACA) Sani Aliyu ya bayyana cewa mutane 81,481 ne ke dauke da cutar Kanjamau a jihar Ondo.

Ya ce bincike ya nuna cewa cikin mutane 81,481 din dake dauke da cutar a jihar mutane 10,000 ne kawai ke zuwa asibiti don karbar magani.

Aliyu ya fadi haka ne a ziyara da ya kai wa sarkin Osemawe Victor Kiladejo a jihar.

Ya bayyana cewa gudanar da wannan binciken zai taimaka wa gwamnati wajen tsara hanyoyin kawar da cutar da sauran cututtuka kamar su Hepatitis B da C kafin nan da shekara 2030.

Ya ce a dalilin haka ya sa suke neman goyan bayan sarkin domin samun nasarar gudanar da wannan bincike.

Sarkin ya tabbatar wa hukumar cewa masarautar sa za ta basu goyon baya matuka domin samun nasara kan abin da suka sa a gaba. Shima kan sa kwamishinan kiwon lafiya na jihar Wahab Adegbenro ya ce gwamnatin jihar za ta mara wa hukumar baya bisa haka ita ma.

Share.

game da Author