Kotu ta warware auren mijin da matar sa ta kaurace masa na shekara biyu

0

Wani magidanci mai suna Wahab Olabanmiji ya maka matar sa Tawakalitu a kotun dake Mapo a Ibadan jihar Oyo yana zarginta matarsa da aikata zina da laifin kaurace masa.

Ya ce haka kawai Tawakalitu ta fara kaurace masa sannan duk da kokarin karkato da hankalin ta da yayi abin bai haifar da da mai ido ba.

” Shekaru biyu kenan matata ta na kin kwanciya da ni sannan hakan bai hanata kwana da wasu mazajen a waje ba.

Ya kuma ce Tawakalitu na muzguna wa ‘ya’yan matarsa na fari wanda a dalilin haka yake rokon kotun da ta warware auren su saboda shi ya gaji haka da auren.

Tawakalitu ta musanta aikata haka, ta ce tun da ta kaurace wa mijinta na tsawon shekaru biyu babu namijin da ya taba ta.

Ta ce ta kaurace wa mijinta ne saboda kwana da tsofaffin matan da yake yi.

” Wata ma’aikaciyyar asibiti ne ta bani shawarar na kaurace wa mijina domin samun kariya daga kamuwa da cututtuka.”

Alkalin kotun Ademola Odunade ya warware auren Wahab da Tawakalitu sannan ya baiwa matar daman rike ‘ya’ya biyu da suka Haifa.

Odunade ya ce Wahab zai rika biyan Naira 6,000 duk wata domin kula da ‘ya’yan.

Share.

game da Author