Za a fara yin fidar Zuciya a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello

0

Shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, Lawal Khalid ya bayyana cewa asibitin ta kammala shiri tsaf domin fara yin fidar zuciya.

Khalid ya fadi haka ne a Shikka – Zariya da yake zantawa da manema ranar Alhamis.

Khalid yace likitocin asibitin za su fara gudanar da wannan fida ne tare da hadin guiwar likitocin asibitin koyarwa na jami’ar Ghana da na Enugu.

” Wannan shine karo na farko da asibiti a yankin Arewa zai fara yin irin wannan fida a Najeriya.
Wannan nasara da muka samu ya biyo bayan shekaru da dama da muka yi muna bincike da shiri domin haka.

A karshe ya ce babbar matsalar da suke yawan fama da shi sun hada da rashin kayan aiki da kudin yin harkokin yau da kullum.

” Duk da wadannan kalubalai da muke fama da su za mu ci gaba da kula da kiwon lafiyar mutane iya karfin mu.” Inji Khalid.

Share.

game da Author