Yadda jami’an tsaro suka farfasa mana Kekuna, suka debe mana kudade a Abuja

0

Direbobin baburan Keke Napep sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa haka kawai jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, ma’aikatan ‘Civil Defence Corps, VIO suka far musu a Unguwar Life Camp ranar Laraba.

A dalilin haka suka fusta suka tottoshe hanyoyi tun daga Jabi har zuwa Karmo.

Daya daga cikin masu Keke Napep din ya shaida cewa an farfasa babura sama da 50 dsa bama aiki suke yi ba suna ajiye na a wuri daya.

” Ba ma a tituna ska same mu mun aikai ba, Baburan na ajiye ne waje daya suka zo suka hau farfasa su har ya kai ga a wasu ma sun bude inda ake ajiyar kudi suka kwashe wa mutane kudaden su.

” Duk inda doka ta bamu damar yin aikin mu muna zama a wurin amma hakan ba ya hana jami’an tsaro musamman VIO muzanta mana ba. Idan sun kama direba sai su kaishi ofishin su dake Wuye su karbi Naira 8,000 daga hannun sa kafin su sakan masa babur din sa.

Ma su Keke NApep din sun roki gwamnati da ta kawo musus dauki domin kuwa abin ya fara fin karafin su.

” Kullum suka zo sai su ce minista ne ya aiko su. Amma kuma ba hana mu suke yi ba kawai har da sace mana kudade. Da karfin tsiya sukan balla mana inda muke ajiye kudi su kwashe kudin mu. Sannan kuma bayan haka su Idan kama ka suka yi shima baka tsira ba.

” Ni dai sun sha kwace mini kudi. Ku in basu ko su nemi kwace mini keken gabadaya.”

Sai dai kuma VIO din sun karyata masu tuka baburan, sun bayyana cewa a dalilin karya doka da suke yi yasa sukan yi farautar su a wasu unguwannin Abuja.

Share.

game da Author