Fadar Shugaban Kasa ta ankarar da jama’a cewa kowa ya yi kaffa-kaffa da kuma taka-tsantsan domin wasu na yin sojan-gona da sunan Yusuf dan Shugaba Muhammadu Buhari a cikin shafunan sada zumunta na yanar gizo.
Sanarwar ta jaddada cewa Yusuf ba ya amfani da kowace irin shafi na sada zumunta a yanar gizo.
Femi Adesina, Kakakin Yada Labaran Shugaba Buhari ne ya bayyana haka inda ya ja hankali da wani shafin instagram da aka bude da sunan Yusuf Buhari mai suna ‘@ymbuhari’.
Daga nan sai ya ce Yusuf Buhari ba ya amfani da kowane shafin zumunta don haka a yi watsi da duk wani shafi da aka ci karo da sunan sa.
Wannan ya na nufin kenan Yusuf ba ya amfani da twitter, facebook, instagram, da sauran su.
Daga nan ya gargadi masu bude shafukan da sunan Yusuf cewa abin da suke yi babban laifi ne, su daina kafin a kure musu gudu.