Sojojin Najeriya sun daka wa wasu gungun ‘yan Boko Haram kashi, yayin da suka yi kokarin kai hari a kauyen Gashigar da ke cikin Karamar Hukumar Mobir, ta jihar Barno, a ranar Laraba da ta gabaya,
Kakakin Yada Labaran Sojoji, Texas Chukwu, yace maraha cike da motocin yaki guda tara dauke da masu manyan bindigogi ne suka suka kai harin.
Sai dai kuma ya kara da cewa sojojin ‘Operation Lafiya Dole’ na Bataliya ta 145, sun kore su.
Ya ci gaba da cewa binciken su ya nuna cewa an kashe Boko Haram da dama, wasu masu yawa sun ji ciwo, inda hakan ta sa tilas suka tsere, kowa ya bazama cikin jeji.
Chuku ya ce bayan an yi gumurzun, sojoji sun sake taruwa wuri daya, inda suka keta cikin dadin Gashigar su n a farautar sauran burbushin Boko Haram.
“Mu na kira ga jama’ar Karamar Hukumar Mobir su kwantar da hankulan su, domin jami’an mu za su ci gaba da tsare rayukan su da dukiyoyin su.” Inji Chukwu.