‘Yan sanda sun damke wanda yayi barazanar kashe Atiku Abubakar da iyalan sa

0

Rundunar ‘Yan sanda ta bayyana damke wani mutum da yayi barazanar kashe tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da iyalan sa.

An kama Augustus Akpan ne dan shekara 43, a Lagos, da jami’an tsaro duka bi diddigin gano inda ya ke, ta hanyar amfani da na’urar gane duk inda wata wayar selula ta ke.

Wayar da aka kama shi da ita, ita da ce ya yi amfani wajen tura wa Atiku sakonnin tes na yi masa barazana shi da iyalin sa.

Cikin makon jiya ne Atiku ya kai korafi ga hukumar ‘yan sanda cewa akwai masu yi wa ran sa da na iyalan sa barazana

Amma Akpan ya shaida wa ‘yan sanda cewa barazanar da ya yi wa Atiku tada-kura ce kawai da kuma burga, ba wai saboda siyasa ba.

Kakakin Yada Labaran ‘yan sanda na tarayya, Jimoh Moshood, ya ce wanda ake zargin ya sha yi wa mashahuran jama’a barazana ya na damfarar su makudan kudade.

Don haka ya ce nan ba da dadewa ba za a gurfanar da shi a kotu.

Kakakin Atiku ya ce ba zai yi wata magana a kan kama wanda ya yi wa wa Waziri na Adamawa barazanar ba.

Ga kadan daga cikin kalaman barazanar da ya yi wa Atiku a cikin tes din da ya tura masa:

“Atiku ka san cewa mu na bibiyar duk wani taku da ka ke yi da kuma duk wani motsi da ka yi – daga kai har sauran iyalan ka gaba daya. Mu na ba ka umarni yanzu-yanzu cewa ka janye takarar shugabancin kasa da ka ke yi.

“Idan ba ka janye ba kuwa, to za mu kashe ka kuma mu yi wa matar ka da ‘ya’yan ka mata fyade. Za mu yi wa ‘yar ka Maryam da ke aiki a CBN fyade, sannan mu nakasa ta kuma mu kashe ta.

“Ita ma ‘yar ka Fatimah da ta yi kwamishinar lafiya a jihar Adamawa, duk mu na da kowane bayanai na sirri a kan ta, sannan mu na da hotunan ta inda ta ke tsirara. Ita da matar ka Jennifer duk za mu tona musu asiri.

“Ka janye daga takara, ka bar Buhari ya yi takara da sauran ‘yan takarar PDP. Saboda mun san ka fi sauran ‘yan takarar karfi sosai.

“Za mu tarwatsa jirgin saman ka, za mu sa maka guba a abinci, ka ci ka mutu kai da iyalan ka. Mun kuma san inda ‘ya’yan ka ke zuwa, duk za mu bi mu kaddamar musu.”

Akpan ya aika da irin wannan sako da wasu bayanai na cin mutunci da tozartawa.

Share.

game da Author