Idan ba a manta be yau Alhamis ne ake gudanar da kareshen zaben jihar Osun da bai kammalu ba.
Mutanen mazabun sun fito domin kada kuri’a.
Dan takarar gwamnan jihar Osun na jam’iyyar SDP, Omisore ya bayyana cewa jam’iyyar APC zai yi a zaben da za ayi ranar Alhamis a jihar.
Idan ba a manta ba shine ya zo na uku a zaben da aka yi ranar Asabar a jihar da jam’iyyar PDP ta lashe zaben da bambamcin kuri’u 345.
Sai dai kuma hukumar zabe ta sanar cewa zaben bai kammalu bu ganin cewa kuri’un da aka soke sun fi yawan bambamcin da aka samu tsakanin APC da PDP.
Wadannan yankuna da za a yi zabe yankuna ne da Omisore yafi sauran ‘yan takarar sanuwa da tasiri wanda a dalilin haka APC da PDP suka fara zawarcin sa tun bayan sanar da cewa za a sake zabe a wadannan yankuna.
Omisore dai ya bayyana cewa zai mara wa jam’iyyar APC ce baya a zaben don samun nasara.
Karanta: ZABEN OSUN: Dalilan Da Ke Sa INEC Cewa Zabe Bai Kammalu Ba






MAMAYAR ’YAN-TA-KIFE A MAZABAR OROLU
A yau an gamu da rincimi a Orolu yayin da wasu ‘yan-ta-kifen jagaliyar siyasa suka mamaye wurin zabe.
Wakilinmu ya lura da cewa masu kada kuri’a na jin tsoron fita jefa kuri’a kamar yadda ya rika ganin jama’a a gefen titi su na tattauna matsalar gungu-gungu.
Daga kuma ‘yan-ta-kifen jagaliyar siyasa din ne suka haifar da soke wasu kuri’u a Orolu a ranar Asabar da ta gabata, abin da janyo aka sake zabe a yankin da abin ya shafa a yau.
A ranar Asabar din, ‘yan jagaliya sun saci akwatai da dama har INEC ta soke zaben.
An kama wakilin PREMIUM TIMES, an sake shi
‘Yan sanda sun kama wakilin PREMIUM TIMES da ke dauko labarai da bayanan wainar da ake toyawa a zaben gwamnan jihar Osun.
An kama Kemi Busari a yau Alhamis.
An kama shi ne a bisa dalilin ya dauki hotuna a rumfar zaben-raba-gardama da ke gudana yanzu haka a Rumfa ta 1, Mazaba ta 8 da ke cikin Karamar Hukumar Urlu, jihar Osun.
Busari na daya daga cikin ‘yan jaridar da aka tantance su dauko labarai na yadda zaben ke gudana, tare da hadin guiwa da kungiyar kare dimokradiyya ta CDD.
An damki wandon Kemi, aka je da shi ofishin ‘yan sanda da ke kusa da wurin zaben, amma kuma nan da nan aka bada umarnin a sake shi.
Tuni Kemi ya koma bakin aiki a filin zabe, ya na aiko da labarai.
INEC ta nuna damuwa kan yadda ‘yan sanda ke wa ‘yan jarida barazana
Ganin yau ne za a yi ta ta kare, inda za a bayyana wanda yay i nasar a zaben gwamnan jihar Osun, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, ta nuna damuwar ta kan yadda ‘yann sanda ke takura wa manema labarai masu bibiyar yadda zabukan ke gudana a rumfunan da ake kada kuri’ar raba-gardama a jihar Osun.
INEC ta ce ta nab akin cikin yadda ta rika samun rahotannin yadda jami’an tsaro ke takura wa ‘yan jarida a wurare da dama, sun a hana su gudanar da ayyukan da dokar kasa ta amince su yi a wurin jefa kuri’a.
Kokarin jin ta bakin kakain yada labaran sojoji da na ‘yan sanda ya ci tura, domin ba wanda yay i magana a kan wannan korafi da INEC ta yi musu.
An samu rahoton inda sojoji da ‘yan sanda suka tozarta jama’a inda rahotannin suka rika yawo a kafafen yada labarai na soshiyal midiya.
Ko a yau Alhamis, ‘yan sanda sun kama wakilin PREMIUMTIMES, Kemi Busari a Karamar Hukumar Orlu, amma daga baya suka sake shi, don kawai ya dauki hotuna a wurin jefa kuri’a.