Mazaunan garin Kubwa dake babbar birnin tarayya Abuja sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa fashe-fashen duwatsun da kamfanin Zeberced ke yi a unguwannin na hana su sakat a gidajen su.
Mazauna sun bayyana cewa fashe fashen duwatsu da wannan kamfani ke yi na matukar cutar da su musamman kiwon lafiyar su.
Wani mazaunin wurin mai suna Abiodun Akanni ya bayyana cewa tun da ya dawo zaman wannan unguwa da iyalen sa dan sa mai suna Livingstone ya kamu da ciwon ido.
” Gidajen mu na gab da rugujewa sannan gaba daya mu da ‘ya’yan mu a takure muke matuka.
Akanni ya ce ‘ya’yan su a takure suke a dalilin wannan aiyukka da kamfanin ke yi.
Ita ma mai makarantar firamaren ‘King’s Gems Montessori’ Mojisola Oladele-Joseph ta bayyana cewa aiyukkan da wannan kamfani ke yi a unguwar su ya shafi aiyukkan da take yi a makarantar ta domin kuwa fashe-fashen duwatsun ya hana daliban ta mai da hankali a karatu.
Bayan haka shugaban kungiyar mazaunan Kubwa Moses Anyaocha ya ce babu irin fadi-tashin da ba su yi ba game da wannan matsala.
Anyaocha yace sun yi kokarin tattaunan da masu kamfanin Zeberced domin samun mafita amma hakan bai haifar musu da da mai ido ba.
Ya ce da abubuwa suka ki sai suka shigar da kara a ofishin ‘yan sandan dake unguwar da kuma ofishin hukumar hako ma’adinai dake Abuja amma duk haka babu abin da akayi a akai.
Anyaocha ya ce a dalilin haka ne muke kira ga gwamnati da ta kawo mana dauki.
Tevarshima Adongo, ya bayyana cewa tabbas akwai illa matuka shakar wannan kura da mutanen yankin ke yi musamman ga kiwon lafiyar su.
” Irin nakiyar da ake saki wajen fasa dutse kan kurmatar da mutum baya ga rashin lafiya da zai yi ta fama da shi.
Adongo ya yi kira ga gwamnati tsawata wa wadannan kamfanoni ko don sabi da kiwon lafiyar mutanen wannan yanki.