Yawan dogaro da tallafi na hana kasashen Afrika ci gaba- Jim Kim

0

Shugaban babban bankin duniya Jim Kim ya bayyana cewa kasashen dake ci gaba za su bunkasa ne idan shugabanin su suka maida hankulan su wajen inganta rayukan mutanen kasashen su.

Ya fadi haka ne a taro da aka yi a kasar Amurka a wannan makon.

Kim ya bayyana cewa kasashen da ke ci gaba za su iya bunkasa ne idan suka daina dogaro da tallafin da suke samu kawai.

Ya ce hakan zai yiwu ne idan gwamnatin wadannan kasashe sun mike tsaye sun fara kula da al’amuran mutane yadda ya kamata.

” Inganta aiyukkan noma, kiwon lafiya, ilimi, samar wa mutane aikin yi da sauran su na daga cikin hanyoyin da zai inganta wadannan kasashe.

Share.

game da Author