Shugaban hukumar fida zakka na jihar Sokoto Lawal Maidoki ya bayyana cewa hukumar su ta tallafa wa kiwon lafiyar tallakawa da gajiyayu da Naira miliyan 7.4 a jihar.
Maidoki y ace hukumar su ta amince da haka ne musamman yadda gwamnatin jihar ke tallafa musu da Naira miliyan 31.5 duk wata domin agaza wa rayuwar talakawa da gajiyayu a jihar.
” A bisa wannan dalilai ne muka raba wannan kudaden wa asibitoci,kungiyoyin da muka hada hannu da su da shagunan siyar da magunguna domin tallafa wa wadanda basu da karfin samun kiwon lafiyan da suke bukata.”