An dora laifin ‘gargizar kasar’ Abuja kan gina rijiyon burtsatse barkatai

0

Kwamitin da Shugaban Kasa ya kafa domin gano musabbabin jijjigar kasar da aka yi a Abuja, makonni biyu da suka gabata, ya dora laifin faruwar ta a kan yawan hakar rijiyoyin burtsatse barkatai da ake yi a garuruwan da ke gefen Abuja.

Mazauna yankunan Jabi, Gwarimpa da Mpape ne suka fi jin wannan jijjiga da kasa ta rika yi a kai akai har kwanaki biyu, Alhamis da Juma’a, 5 zuwa 7 Ga Satumba.

Duk da cewa ba wannan ne karo na farko da aka fara jin wannan jijjiga ba. Wannan da ta faru baya-bayan nan ta tayar da hankulan mutane sosai, kasancewa har cikin Abuja an rika jin jijjigar, musamman a a Maitama da kuma Garki.

Tun bayan faruwar lamarin dai Ministan Abuja Bello Mohammed ya hana gina rijiyoyin burtsatse, fasa duwatsu da sauran hakar ma’adinai a Abuja, musamman a yankin Mpape inda aka bayar da rahoton jijjigar ta fi karfi sosai.

Garin Mpape dai a kan tsauni ya ke, kuma kewaye ya ke da manya-manyan tsaunuka da suka kewayec Arewaci da Gabacin Abuja.

Bayan faruwar jijjigar, an kafa kwamitin bincike a karkashin jagorancin Shugaban Hukumar Binciken Sararin Samaniya, Seidu Mohammed, wanda ya mika rahoton sa a yau Juma’a.

Sai dai kuma wasu mazauna yankunan sun nuna tsoro da kuma fargaba cewa jijjigar kasar da aka yi ta na da nasaba ne da yawan fasa duwatsu da ake yi a yankin Abuja, ba gina rijiyoyin burtsatse ba.

Kwamitin bincike ya tabbatar da cewa sun gano wasu wuraren da aka gina rijiyoyi na da nasaba da faruwar jijjigar kasar, wadda ta jijjiga hankulan mazauna Abuja da kewaye.

Yayin da kwamitin ke mika rahoton sa ga Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya bayar da shawar cewa gwamnati ta tsaurara matakan ayyukan da suka jibinci hakar duwatsu, rijiyoyin burtsatse da sauran ma’adinai a Abuja.

Daga nan sai kwamitin ya danganta jijjigar kasar da aka yi cewa ta faru ne sanadiyyar yadda a kullum ake kwalkwalar ruwa akalla metirik tan har 330,000 a Abuja da kewaye.

Kwamitin ya kara da cewa idan gwamnati ba ta yi hanzari ba, to irin wannan girgizar kasar za ta ci gaba da faruwa a Abuja, saboda yawan gina rijiyoyin burtsatse da ake yi barkatai.

Shugaban Kwamitin, Seidu Mohammed ya bayyana cewa akwai akalla rijiyoyin burtsatse 110,000 a Abuja da kewaye.

Rahoton ya nuna cewa yankin garin Mpape mai tsaunuka ne ya fi zama cikin barazanar yiwuwar girgizar kasa.

Haka nan kuma kwamitin ya tunatar da cewa wani rahoto da kamfanin Julius Berger ya bayar bayan ya gudanar da bincike, ya bayyana cewa yankin Mpape mai tsaunuka ba shi da karfin karkashin kasa sosai.

Tsandaurin karkashin kasar yankin ba shi da karfin rike jijiyoyin da suka rike farantin da ke tallabe da karkashin kasar baki daya.

Rahoton wanda Julius Berger ta fitar tun cikin 1978, ya nuna cewa yankin Mpape na daga cikin yankin da ake kira ‘Shear zone’ a duniya, wato inda ke fuskantar gafcewar girgizar kasa.

Idan ba a manta ba, bayann faruwar jijjigar kasar, gwamnati ta bayar da tabbacin cewa kowa ya kwantar da hankalin sa, jijjigar kasa ce, ba girgizar kasa ba.

PREMIUM TIMES a lokacin ta ruwaito cewa, Hukumar Agajin Gaggwa ta Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta bayyana cewa babu alamomin yin girgizar kasa a cikin Abuja da kewaye, kamar yadda aka Ji kasa ta yi jijjiga wasu yankuna, musamman a Mpape da kewayen unguwannin gefen ta.

An dai ji wannan jijjigar kasa ne a ranar Laraba da dare zuwa Alhamis da safe, a Abuja, ciki kuwa har da yankin Gishiri Junction, NICON Junction da sauran wurare.

Wannan jijjiga dai ta razana mazauna yankunan sosai.

KADA A TAYAR DA HANKULA -Inji NEMA, kafin bincike

Sai dai kuma Daraktan hukumar NEMA, Abass Idris, ya ce ba abin tayar da hankula ba ne.

A wata hira da ya yi da NAN, a yau Juma’a, ya ce jijjigar kasar da aka ji a yankin Mpappe da wasu wuraren ciki har da Maitama, ba ya nufin akwai yiwuwar yin girgizar kasa a Abuja.

Ya ce wannan jijjiga ba ta rasa nasaba da wani irin karamin rugugin motsawar jijiyoyi ko igiyoyin da ke rike da kasa mai yiwuwa su tsinke yayin da motsawar ta wakana.

Wannan kuma inji shi, ba zai haifar da yiwuwar girgizar kasa ba.

“Lokacin da jami’an mu suka je wajen mazauna yankin Mpape, sun samu tabbacin cewa ba a wannan ne karon farko da hakan ta taba faruwa ba.

Sun ce an taba yin wannan jijjigar kasa shekaru biyar da suka gabata.”

Sai dai kuma ya ce akwai bukatar a duk lokacin da hakan ta faru, to mazauna yankin su gaggauta ficewa su sake wuri, kafin jijjigar ta lafa.

Ya roki mazauna yankin idan sun ji irin haka, to su shige a karkashin tebura su boye idan su na cikin daki ne.

Ya ce kuma a kauce daga jikin tagogi ko kyauren dakuna a lokacin da kasar ke jijjiga.

Sannan kuma kada a tsaya kusa da gine-ginen gidaje, ko karkashin manyan bishiyoyi da turakun wutar lantarki.

Wani mazaunin Maitama mai suna Victor Okoye, ya ce da ya ji rugugin kara ya dauka dutsi ne ake fasawa, amma sai ya ji wannan rugugin ya fi karfin fasa dutse.

“Ai da na fito daga gida sai na fahimci dai kasa ce ke jijjiga. Nan fa hankali na ya ba ni cewa, ai shikenan, tashin duniya ya zo.”

Wata mai suna Alice Adetola da ke Mpape kuwa, ta razana kwarai da gaske, ta ce haka su ma yaranta.

“Tashi na yi na rungume yara na, ina ta buga addu’a, domin na dauka ba za mu kai gobe ba.”

ALAMOMIN AFKUWAR GIRGIZAR KASA A ABUJA -Daraktan Gine-gine

Darakta Janar Danladi Matawal na Cibiyar Binciken Gine-gine da Titina, ya yi gargadin cewa kada fa Najeriya ta yi wa afkuwar jijjigar kasar da ta faru a Abuja rikon-sakainar-kashi.

Cikin wani bayani da ya fitar, ya ce tabbas akwai bukatar gwamnati ta gaggauta binciken musabbabin faruwar wannan jijjigar kasa a Babban Birnin Tarayya, Abuja, wadda ta afku a sassan Abuja a ranakun Alhamis da Juma’a.

Ya ce akwai bukatar Najeriya ta fito da tsarin da zai magance sake faruwar wannan jijjigar kasa, ya-Allah ko dalilin hakar kasa ne ta faru ko kuma a’a.

“In dai akwai inda aka rarake karkashin kasa ana gina titin karkashin kasa ko yin wani gini a karkashin kasa, to wannan gini kan iya kumbura jijiyoyin kasa har su fara jijjiga.” Inji Matawal.

“Su kan su mazauna Abuja na matukar bukatar da a horas da su matakan gaggawar da ya kamata su dauka a cikin hanzari, idan irin haka ta sake kasancewa.

“Idan wannan jijjiga kaddara ce daga Allah Ta’ala, to fa sai a yi shirin fara kwashe mutane daga Abuja ana ficewa, domin ita babbar girgizar kasa fa ta kan fara ne da ‘yar jijjigar kasa, dalili, saboda karkatsewa da daddatsewar da igiyoyi ko jijiyoyin karkashin kasa ke yi ko kuma saiwa-saiwar da ke rike da farantin da ke tallabe da jijiyoyin karkashin kasar su kan su.” Gargadin Matawal kenan.

“Wato aman wutar duwatsu da girgizar kasa duk wani balbalin bala’i ne wadanda Najeriya ba ta ma taba tunanin yi musu shirin ko-ta-kwana ba. To saboda ba a taba shirya musu din nan ba, sai jikin mu ke ba mu cewa kamar ba mu ma san da su ba, ko kuma ba mu yarda za su iya faruwa a nan ba.”

“Zan ja hankalin mu da cewa wani ya ba mu labari cewa a inda ya ke a garin Mpape, inda jijjigar kasar ta fi karfi, kare ya fara ji ya na ta haushi ba kakkautawa. Jin haka sai mu ka yi ta rafka addu’a cewa Allah dai ya sa wannan abu ba wani ibtila’i ba ne daga Allah.

“Domin idan ibtila’in girgizar kasa ce, to gargadin farko da jama’a za su fara ji shi ne dabbobi su fara firgita su na haushi, su na fafarniya.

“Za a ga karnuka sun kaure da haushi ba kakkautawa, maguna su kasa zaune, su kasa tsaye wuri daya, su na ta sagarabtu, beraye su rika gig-gilmawa cikin gida ko cikin dakuna a guje, kuma a rude. Dawaki kuma su rika harbin iska da haniniya su na fizge-fizgen tsinkewa daga turakun su, su na fagamniya a rude.”

“Ba wani abu ba ne zai sa su rika yin wannan sai saboda maganadison ji da sauraren su ya sinsino kuma ya fizgo musu karkarwar da karkashin kasa ke fara yi a lokacin da jijiyoyin karkashin kasa ke daddatsewa daga jikin farantin da ke tallabe da karkashin kasar baki daya.”

Ya ce mataki mafi sauki da kuma saurin dauka idan irin haka ta faru, to a yi gaggawar ficewa daga inda ake, a kwashi yara da kananan dabbobin da za a iya runguma, a runtuma a guje zuwa cikin fili ko sararin da babu gine-gine kusa.

Matawal ya ci gaba da bayar da wasu misalai da alamomin matakai har guda hudu masu nuni da cewa idan hakan ta auku, ko kuma ta fara aukuwa, to babu makawa girgizar kasa na tafe.

Share.

game da Author