Kokawar darewa kujerar gwamnan Jihar Osun kai tsaye daga wakilan mu…
Zuwa karfe 10 na safiyar Asabar din yau, daruruwar mutanen jihar Osun sun fito domin a tantance su.
A wasu rumfunar zaben ma har an fara kada kuri’a.
Komai dai na gudana cikin natsuwa da kwanciyan hankali.


Manyan jam’iyyun siyasa da ke fafutikar kokawar nasara a zaben gwamnan jihar Osun da ke gudana yau Asabar, sun shigo da sabbin dabarun sayen kuri’u daga hannun masu zabe.
Maimakon su rika raba kudi a sarari a wuraren jefa kuri’a, jam’iyyun sun sake dabarar rika rubuta sunayen wadanda suka jefa ko za su jefa musu kuri’ar, daga baya su biya su.
A kwanakin baya ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana soke amfani da wayar selula a cikin akurkin jefa kuri’a, ya ce ta yi hakan domin dakile harkallar saye da kuma sayar da kuri’u a ranar zabe.
Sai dai kuma wakilnan PREMIUM TIMES da ke lura da yadda zabe ke gudana a wurare daban-daban a jihar Osun, sun ga yadda aka shigo da wasu dabarun sayen kuri’a da sayar da ita a wurin zabe.
A wata mazabar Karamar Hukumar Ede ta Arewa, akwatin Unit 2, na mazabar 11, an ga wani ejan na jam’iyyar APC ya na rike da wata takarda da biro, wanda ya ke rubuta sunayen wadanda suka rigaya suka jefa kuri’a.
An kuma lura da yadda ya kan rika yin farat ya na kebewa wani wuri ya na karbar sunayen na su.
PREMIUM TIMES ta samu daukar muryar maganganun da mai rubuta sunaye da masu bada sunayen na su ke yi.
“Ka kuwa rubuta suna na?” Haka wata mata mai matsakaitan shekaru ta yi tambaya.
“Haba dai, na rubuta sunan ki mana. Ki je, ma hadu an jima.”
Sai dai kuma wakilinmu bai samu jin sunan mai daukar sunayen wadanda suka yi zaben ba.
Wakilan mu sun gano cewa an yi haka a rumfuna da dama, kuma har PDP da APC sun shiga cikin wannan daka-dakar.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=YL-SjHWwsAY&w=560&h=315]
A mazabun Unit 3, 5,4 duk wakilinmu ya ga ejan-ejan na APC da takarda da biro a hannayen su.
Wadanda suka san irin wainar da ake toyawa bayan karbar sunayen wadanda suka kada kuri’un su, sun bayyana wa wakilin mu cewa bayan an gama ana bin sunayen ne daya bayan daya ana kira an aba su dan hasafin kudade.
“Ba mu san ko nawa za a ba mu a wannan zaben ba. Amma dai a zaben baya, naira 500 aka rika ba kowa. A wasu wuraren kuma an ce har naira 2,000 an rika bayarwa.”
A rumfar zabe 005 da ke mazabar Ileeogbo kuwa, da idon wakilin mu ya ga ejan din wata jam’iyya na raba kudade a Karamar Hukumar Ayedere.
Wasu na cewa naira 2,000 ya kamata a ba su, amma an ba kowanen su naira 500.
Jami’an tsaro kuma sun kama wasu kananan yara biyu a wurin zabe, amma daga bisani aka bar su sukadangwala kuri’u suka yi gaba.
KOWANE GAUTA JA NE
Jam’iyyu 48 suka shiga takarar zaben gwamnan jihar Osun. Sai dai kuma akwai manyan ‘yan takara guda fiyar fitattu da ake wa lakabi da “Fulogan Osun Biyar”, wadanda aka yi ittifaki cewa daga cikin su ne gwamnan jihar zai fito.
Akwai Ademola Adeleke na PDP, Gboyega Oyetola na APC, Iyiola Omisore na SPD, Fatai Akinbade na ADC da kuma Moshood Adeoti na ADP.
Dukkan wadannan Fulogai Biyar, kar-ta-san-kar ne, sun yi gumurzun adawa da gabar siyasa a tsakanin su. Kafin fitowar su wannan takara, dan takarar ADC da na SDP duk manyan jiga-jigai ne a cikin jam’iyyar PDP, kafin su fice.
Haka shi ma Adoeti, ya sauka mukamin Sakataren Gwamnatin Jihar Jihar Osun a karkashin gwamna Rauf Aregbesola.
Shi kuwa Adeleke, a baya jigo ne a jam’iyyar APC, har zuwa cikin Mayu, 2017 inda fice a fusace, ya tsaya takarar zaben cike gurbin sanata Isyaka Adeleke, yayan sa wanda ya mutu ya na kan mukamin sanata a karkashin jam’iyyar PDP. Adeleke ya yi nasarar hawa kujerar yayan sa, amma a kan jam’iyyar PDP.
Su ma kananan jam’iyyu sun yi kokarin kaiwa ga masu jefa kuri’a domin neman goyon baya, amma irin kamfen din da manyan Fulogan Osun Biyar din nan suka yi, ya dakushe kaifin makaman su, kuma ya dusashe hasken kuzarin su.
Shi ya sa ake kallon sauran jam’iyyun 43 a matsayin taron yuyuyu, ko ma a ce tsintsiya ba shara. Ba wai don ba su cancanta ko ba su da kyakkyawar alkibla ba ce, sai don kawai abin da Hausawa ke kira, ‘Mai hannu da shuni, shi ake bai wa murjin zare.’
Su kuma manyan Fulogan Osun din Biyar, kusan duk kudirorin su da alkawurran su iri daya ne. Ko dai alkawarin inganta tattalin arziki, lafiya, harkar noma ko kuma inganta ababen more rayuwar al’umma. Sun kuma yi alkawarin share hawayen rashin biyan albashi da alawus din ma’aikata da aka dade ba a ci oriyar su ba da dadewa a jihar.
Dan takarar APC ya dan samu tagomashi makonni kadan kafin zabe, a lokacin da gwamnatin jihar ta fito da kudaden fara biyar kwantai din albashin ma’aikata da aka dade ba a biya ba.
Sai dai kuma dukan kirjin kasassabar da jigon APC na kasa, Bola Tinubu ya yi a wurin kamfen din dan takarar gwamnan a karkashin APC, ya rage masa goyon baya matuka.
Bola Tinubu ya ce ya fi jihar Osun gaba dayan ta arziki da dimbin dukiya, don haka shi bai ga abin da zai tatsa a jikin nonon saniyar Osun ba.
A yau ne dai za a yi ta ta kare, domin shi dai mai zabe a jihar, ya san wanda zai zaba a cikin ran sa. Yau Asabar alkiyamar siyasar wasu za ta tashi, ta wani kuma ta tsaya.
OMISORE: DAN NA IYA KA FI DAN NA GADA
*Omisore kwararren dan siyasa ne, domin ya taba rike mukamain mataimakin gwamnan jihar, kuma ya taba yin sanata. Sai dai matasalar sa it ace, jam’iyyar da ya ke takara a karkashin ta, SDP, ba ta da karsashi kamar na sauran jam’iyyar PDP na APC a jihar. Amma duk da haka ba a nan ta ke ba, wai an danne budari ta ka. Komai na iya faruwa. Zai iya yin nasara, tunda ya san ‘kan-tsiyar-siyasa’. Sai dai kuma duk wani kulli ko kwance kulli ai kafin zabe ake yin sa, ba a ranar zabe ba.
ADELEKE NA PDP: KO GWANIN RAWA ZAI FADI?
Dan takarar DPD Adeleke ba sabon shigar siyasa ba ne, duk da ya ke dai ya na takama da cin gado ko cin albarkacin yayan sa, marigayi Isyaka Adeleke. Amma yadda ya fice daga APC mai mulki, ya afka jam’iyyar Adawa, PDP kuma ya ci zaben sanata, to hakan ma a zaben gwamna zai iya firgita jam’iyyar APC. Kuma ko a yanzu din ma a firgicen ta ke.
Gwanin rawa Adeleke, ya na takama da kwarewar sa wajen iya rawa ‘kwambilo’ da rawar ‘adagwashe’, har ma cewa ya yi idan ya ci zabe, da taka rawa ya na tsalle zai shiga gidan gwamnati. Wannan rawa kuma ta na kai masa, domin ta samar masa karin magoya baya sosai.
Duk lokarin da aka yin a shantale masa kafafuwa da batun zargin bai yi jarabawar fita daga sakandare ba, WAEC da sauran kararrakin da aka kai shi, ba su yi tasiri a kan sa ba. Da alamu dai gwanin rawa zai kai labari. Idan ta yi wani juyin kuma, ya ci kasa saboda hajijiyar da za ta hana shi direwa tsaye kyam, idan ya yi wani wawan juyin a sakamakon zaben yau Asabar.
OYETOLA: DAMAR APC KUMA MATSALAR APC
Ana yi wad an takarar APC kallon mutum ne natsatstse kuma kamili, sai dai kawai a ce sabon-yanka-rake ne a cikin siyasa. Duk wani toroko da kwambon da ya key i, da bazar Bola Tinubu ya ke rawa. Wannan kuwa za ta iya rage masa kaifi da tasiri a zaben yau.
Wasu kuma na auna zurfin ruwan cancantar sa da irin rikon da Gwamna Aregbesola ya yi wa jihar Osun. Matsalar rashin biyan albashi na iya zame masa alakakai kokarfen kafa, wanda masu zabe ka iya gudun idan ya hau, zai ci gaba daga inda Aregbesola ya tsaya.
Idan ya ci zaben yau, ba za a yi mamaki ba. Amma idan ya fadi, tabbas za a danganta faduwar sa da irin kuncin rayuwar da gwamnatin Aregbesola ta APC ta jefa ma’aikatan jihar tsawon shekaru uku.
Sauran ‘yan takarar biyu ba kanwar lasa ba ne. Kowa na iya ci, kuma ba za a yi mamaki ba ‘Yan siyasa ne kuma sun san jama’a haka kuma sun shiga cikin su sosai. Haka kuma idan suka fadi ba mamaki za a yi ba. Domin me, shi zabe dama dan takara daya ne ke yin nasara – ko da rata mai yawa, ko kuma da kyar da jibin goshi.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=qgBFb16_hnQ&w=560&h=315]
Omisore ya koka da yadda ake cikinin kuri’u
Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar SDP, Iyiola Omisore, ya nuna damuwar sa dangane da yadda yadda dillalan sayen kuri’u ke cin kasuwar su a wurin zabe.
Ya nuna damuwar ta sa ne bayan da ya jefa kuri’ar sa a mazabar Rufar Zaben Unit 3 ta mazabar 1 da ke Ife ta Gabas.
Omisore, wanda ya taba yin Mataimakin Gwamnan Jihar Osun kuma tsohon sanata, ya isa rumfar jefa kuri’a da misalin karfe 11: 05 na safe. Kuma ya jefa ta sa kuri’ar daidai 11:15 na safe.a lokacin da ya ke wa manema labarai jawabi, ya bayyana cewa ya lura akwai matsaloli tattare dazaben.
Sai dai kuma ya yaba wa INEC dangane da irin kokarin da ya gani dangane da yadda zaben ke gudana.
‘Yan sanda sun saki dillalin cinikin kuri’u
Jami’an ‘yan sanda sun damke wani dillalin cinikin kuri’u, amma daga baya suka sake shi.
Dillalin da ake kira Sunday,an kama shi a Rumfar zabe Unit 3 Mazabar 06 ta Karamar Hukumar Ifedayo.
Da misalin karfe 19:46 na safiya ne aka ga wani mutum tsate a gefen rumfar zabe, ya na tare wanda ya jefa kuri’a ya na tantance sunan sa a cikin wata takarda mai dauke da sunaye.
Duk wanda ya duba, idan ya tabbatar da jam’iyyar ejan din ce, sai ya zaro kudi ya ba shi.
Nan da nan an kira ‘yan sanda inda suka cafke shi tare da wani abokin dillancin sa, kuma aka yi gaba da su.
Sai dai kuma wani abin mamaki shi ne, bayan ‘yan mintina kadan da damke Sunday, sai ga shi ya dawo, kankanin lokaci kadan bayan da shugaban jam’iyyar sa ya dawo.
An dai samu rahotannin cinikin kuri’u a kananan hukumomi da mazabu da dama.
Discussion about this post