Sama da Kauyuka 200 suka gamu da ibtila’in ambaliyar ruwa a jihar Jigawa

0

A wani abin tausayi da juyayi da ya faru a wasu kauyuka sama da 200 a jihar Jigawa ranar Juma’a ambaliyar ruwa ya barnata gonaki, gidaje sannan ya ci rayuka akalla 19.

Hakan ya faru ne a sanadiyyar bude dam din Tiga da aka yi.

Mazauna garuruwan da suka tattauna da wakilin mu sun shaida masa cewa basu taba ganin irin wannan jarabawa ba.

” Gaba daya gonakin mu sun lalace, sannan kusan duka manoman mu sun yi noma ne da bashin gwamnati. Yanzu kaf sun rasa komai.

” Sama da mutane 200 yanzu haka basu da inda za su kwana bayan rasa rayuka da aka yi.

Mazauna garin sun koka kan cewa hukumar NiMet kan sanar dasu a duk lokacin da za a bude wannan dam domin su shirya amma wannan karon basu ce musu komai ba kawai sai suka ga ruwa na malala a ko ina a garuruwan su.

Kananan hukumomi akalla 14 ne suka fada wannan ibtila’i.


Mataimakin gwamnan jihar Jigawa Hassan Hadejia ya bayyana cewa sai da maza-maza suka sa aka kera kwale-kwale sama da 200 bayan wadanda aka kawo musu gudunmuwa domin ficewa da mutane.

” Ni dinnan masunci ne amma na fitar da mutane da dama zuwa asibiti a kwale-kwale na. Wannan abu yayi matukar ta da mana da hankali.” Inji wani mazaunin garin Zogawa.

Mataimakin gwamna ya ce tuni har sun fara raba kayan agaji ga mutanen da abin ya shafa. Sannan kuma mazauna garin sun yi kira ga attajirai da masu hali da su kawo musu dauki.

Share.

game da Author