Mahara sun kashe mutane 8 a jihar Nasarawa

0

Rundunar ‘Yan sandan jihar Nasarawa ta sanar da rasuwar wasu mutane 8 da mahara suka harbe a garin Sofiyo, karamar hukunar Toto.

Kenedy Idris, kakakin rundunar’Yan sandan jihar ya gargadi mutanen jihar da su gujewa daukar hukunci da kan su.

” Tabbas wasu mahara sun kashe mutane 8 a garin Sofiyo. Sannan wasu da dama sun tsira da rauni a jikin su.

” Wadanda suka samu rauni na samun kula a asibitin Gwagwalada.”

Idris ya ce tuni sun tura jami’an lungi-lungu, kwararo-kwararo domin farautar wadanda suka aikata wannan mummunar aiki.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ne ya ruwaito wannan labari.

Share.

game da Author