Hausawa dai sun ce Karya fure take bata ‘ya’ya. Wannan karin magana na yin tasiri ne idan mutum ya binne wata kamayamaya kuma ya nemi ya ci gaba da nuna shi shafaffe da mai ne.
Ministan harkokin kudi na Najeriya Kemi Adeosun ta ajiye aiki a ranar Juma’a a dalilin wani karya da ta binne shekaru da dama tana cin karenta babu babbaka.
Tuni dai har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da wasikar yin murabus din sannan ya umarci karamar miniatan kudi Zainab Ahmed da ci gaba da rike ma’aikatar.
Kemi dai ta rufta cikin kwamacalar satifiket din shaidar yafiya na yin aikin bautar kasa na karya da ta yi ta amfani da shi a tsawon rayuwan ta na aiki kafin jaridar PREMIUM TIMES ta bankado wannan harkalla ta baza wa duniya.
A wasikar ta Kemi ta godewa gwamnatin Buhari kan damar da ta bata na yi wa kasa aiki sannan ta ce satifiket bogi da tayi amfani da shi ba da gangar ta buga shi ba.
” Ni ma ban taba sanin cewa wai wannan Satifiket na bogi bane, domin domin bani aka yi bayan ha zama dole sai na mallaka bayan ba dawo Najeriya.” Inji Kemi.
Idan ba a manta ministan harkokin kudi na Najeriya Kemi Adeosun ta buga satifiket din karya cewa an yafe mata yin bautar kasa NYSC a Najeriya bayan ta kammala Jami’a.
Wannan karya da ta lafta ya tada hankulan mutanen Najeriya matuka ganin cewa gwamnatin da take wa aiki gwamnati ce da ke bugun kirji da yin kururuwar ita gwamnati ce mai tsafta.
Tabbatattu kuma sahihan shaidun bayanai rubutattu sun tabbatar da cewa Ministar Harkokinn Kudi, Kemi Adeosun ba ta yi aikin bautar kasa ba, kuma a lokacin shekarun ta ba su kai na wadda aka dauke wa aikin bautar kasar ba.
PREMIUM TIMES ta gano cewa Kemi ta mallaki shaidar yin bautar kasa ne ta hanyar yin fojare, shekaru da yawa bayan da ta kammala jami’a.
Yan Najeriya sun harzuka sosai bayan fallasa harkallar da Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ta yi, inda ya tabbatar da cewa kiri-kiri ta ki zuwa aikin bautarc kasa wato NYSC, a lokacin da ta kammala babbar kwalejin ta.
Akasarin wadanda suka tofa albarkacin bakin su, sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya kafa kwamitin bincike domin a tabbatar da gaskiya ko akasin gaskiyar wannan labara da PREMIUM TIMES ce ta bankado shi.
Mafi yawan wadanda suka yi rubuce-rubuce a shafunan yanar gizo, sun cika da mamakin yadda hukumomi da jami’an tsaron bincikenn kwakwaf suka kasa gano wannan bahallatsa ta Kemi, har sai da PREMIUM TIMES ta fallasa ta.
Takardun karatun Kemi da ke hannun PREMIUM TIMES sun nuna cewa an ba ta satifiket na yafe mata zuwa bautar kasa a shekarar 2009, a bisa yawan shekaru.
A kwanakin baya, Kakakin fadar shugaban kasa ya fito kakara in da ya shaida wa ‘yan Najeriya cewa tabbas akwai wannan magana kuma gwamnati na dubawa da yin bincike akai. Sai dai kuma ya bayyana cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba zai dauki mataki a kai ba har sai an tabbatar da gaskiyar maganar ta hanyar bincike da suke yi.
Discussion about this post