Sanata Shehu dake wakiltar shiyyar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar sa ta APC da su dawo su hada kai domin tunkarar zaben 2019 musamman a jihar Kaduna.
Sanata Sani ya bayyana haka ne a hira da yayi da gidan talabijin na Channels.
” Mu yanzu rabuwar kai da adawa da juna ba namu bane a jihar Kaduna. APC a jihar na bukatar a zo a hada kai a dinke tamau domin tunkarar zaben 2019 musamman a jihar.
” A wannan karon kusan duka ‘yan siyasan jihar da ke da tasiri matuka da gogewa wajen iya shirya tuggun siyasa da karfi wajen karkato ra’ayin mutane a siyasance duk suna tattare a jam’iyyar adawa.
” Dole ne fa mu hadu wuri daya domin tunkarar su da karfin mu a matsayin tsintsiya madaurinki daya.
Idan ba a manta ba Sanata Shehu Sani da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ba a ga maciji a tsakanin su, watanni kadan bayan an kafa gwamnatin APC a 2015.
Hakan ya sa har tsinuwa da kwashe wa juna albarka sai da aka yi ta jifar juna da.
Yanzu dai dabara ya rage wa mai shiga rijiya domin kuwa tuni gwamna El-Rufai ya halasta babban aminin sa, kuma mai bashi shawara kan harkar siyasa, wato Mal. Uba Sani a madadin Shehu Sani cewa shine zabin sa.
Game da salon mulkin shugaba Muhammadu Buhari, Shehu Sani ya jinjina wa shugaban kasan.
” Buhari ya yi rawar gani a mulkin sa a tsawon Shekaru uku zuwa yanzu. Idan ka duba abinda yayi a cikin wadannan shekarun, dole ka yaba masa.
” Kuma ina tabbatar muku da cewa Buhari ne zai lashe zaben 2019 ko shakka ba na yi domin ko yayi wa kasar na abin azo a agani.