Kotun Ladafta Ma’aikata za ta ci gaba da shari’ar wasu ma’aikatan Jihar Bauchi

0

Kotun Ladaftar da Ma’aikata ta bayyana cewa a ranar 18 da 19 Ga Satumba ne za ta ci gaba da shari’ar wasu ma’aikatan Gwamnatin Jihar Bauchi da ake tuhuma da laifin kantara karyar mallakar kadarori.

An dai fara shari’ar wadanda ake tuhumar a Babbar Kotun Jihar Bauchi, amma daga baya aka maida shari’ar a Abuja bayan da kotun ladaftarwar ta kasa warware tuhumar da ake yi wa wasu da ake zargin.

Kakakin hukumar Ibrahim Alhassan ne ya bayyana haka inda ya ce cikin wadanda ake tuhumar har da wani kwamishina da ke kan mulki a yanzu a jihar Bauchi din.

Ya ce sashen binciken shari’a na hukumar ne ya bayar da ranar da za a ci gaba da sauraron karar, inda Daraktar Sashen, Hajiya Binta G. Abubakar ta sa hannu a kan takardar.

Sanarwar ta ce wadanda ake tuhumar dai su 10 ne, amma za a saurari tuhumar hudu daga cikin su a ranar 19 Ga Satumba.

Dukkan wadanda ake tuhumar dai su na rike ne mukamai na siyasa da gwamnan jihar Bauchi ya nada su.

Za a ci gaba da wannan shari’a ne a hedikwatar kotun da ke Daki Biyu, Gundumar Jabi da ke Abuja.

Share.

game da Author