Ranar Talatar nan ce gwamnatin tarayya ta gindaya wa jihohin tarayyar kasar nan sharuddan da sai kowace ta cika kafin a ba ta sauran cikon kudaden Paris Club tukunna.
Sauran cikon da tarayya za ta raba wa jihohin sun kai kiyasin naira bilyan 823.5, wanda za a ba kowace jiha dala daya a kan naira 306.25.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Kudade ne ya bayyana haka. Hassan Dodo, ya lissafa ka’idojin cewa sun hada da tilas jiha ta bayar da fifiko wajen biyan albashi da kudaden da kuma sauran batutuwan da suka jibinci biyan alawus da kuma kudaden ariyas na ma’aikata da kudaden.
Sauran ka’idojin sun hada biyan lamunin da jihohi suka ci daga gwamnatin tarayya a bisa gudanar da ayyukan da ke cikin kasafin kudin da jihohin suka ce sunn karbi lamunin ne domin su yi ayyukan.
Wadannan lamuni dai ana maganar tun na cikin shekarar 2016. Sannan kuma akwai sharadin biyan kudaden takin zamani da suka karba daga gwamnatin tarayya, a karkashin Shirin Raba Takin Zamani na Ofishin Shugaban Kasa.
An kuma gindaya wa jihohi cewa su nuna da gaske su ke yi wajen kokarin gudanar da ayyukan Hukumar Samar da Ilmin Bai Daya, wato UBEC.
Dodo ya ce wadannan bayanai ne gwamnatin tarayya ke nema daga jihohi domin a san abin da kowace ta yi da kudaden da aka ba ta na baya, ta yadda za a auna cancantar ba ta sauran balas na kudaden Paris Club din da suka rage, wadanda a yanzu aka gindaya mata sharuddan da ake so jiha ta cika kafin samun kudaden tukunna.
Discussion about this post