Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA, ta gargadi jihohi da kananan hukumomi da su gaggauta yin kwakwaran shiri domin kauce wa ambaliya a yankunan su.
Jagoran da Gwamnatinn Tarayya ta nada ya shugabanci kwamitin wayar da kai ga jama’a ne ya bayyana haka a wani taro da aka gudanar a Fatakwal.
Umar Mohammed ya ce makasudin wannan taro shi ne a tsara wa masu ruwa da tsarin da suka halarci taron shirin gaggawa da ya dace kuma ya wajaba a dauka idan har akwai alamun barkewar ambaliya a yankunan su.
Ya roki sauran jama’a su shiga cikin wannan gagarimin aikin wayar da kai da kuma daukar matakan kauce wa barkewar ambaliya.
“Wajibin gwamnatocin jihohi ne su tanadi wuraren fakewa da kuma matsugunai ga wadanda ambaliya ta yi wa barna, domin ita dai ambaliya abu ne da ba mu iya tsayar da ita. Amma fa a mu na iya rage ta, ta hanyar daina toshe magudanun ruwa da manyan hanyoyin da ruwa ke bi ya na wucewa, kwalbatoci da kuma daina yin gine-gine a kan hanyar da ruwa ke wucewa.”
“Jihohi da kananan hukumomi su rika bai wa jami’an NEMA hadin kai ta hanyar gaggauta amsa kiran su idan batu na daukin gaggawa ya taso.”
“A shirye mu ke mu gaggauta zuwa cikin hanzari a duk lokacin da kowace jiha ta kira mu, don haka mu na yin kira ga jihohi da su tanadi wuraren fakewa ga jama’a idan hakan ta taso a cikin gaggawa.’’