Kashi 70 bisa 100 na yaran da aka haifa a jihar Kaduna basu da katin shaidar haihuwa

0

A yau Talata ne jami’ar hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya ta jihar Kaduna Hadiza Balarabe ta koka kan yadda rashin yi wa yara rajista ke kawo wa gwamnati cikas a ayyukan ta.

Ta ce bincike ya nuna cewa mutane jihar Kaduna basu damu da yi wa yaran su rajistan katin shaidar haihuwa ba.

Hadiza ta bayyana cewa rashin yi wa yara rajistar katin haihuwa na kawo wa gwamnati matsala wajen shirin samar da ababen more rayuwa ga mutanen jihar.

” A yanzu haka adadin yawan yaran da basu da takardun haihuwa sun kai kashi 70 bisa 100.

Hakan na nuna cewa gwamnati na samar da ababen more rayuwa wa kashi 30 bisa 100 ne kawai.

Hadiza ta ce amma da taimakon UNICEF gwamnati jihar Kaduna za ta iya samar wa mutanen jihar musamman yara kananan isassun ababen more rayuwa.

” Gwamnatin jihar Kaduna ta hada guiwa da UNICEF don ganin an yi wa yara rajista a jihar.

Bayan haka jami’in hukumar kidaya na Kasa Umaru Adamu ya bayyana cewa jihar Kaduna na fama da matsalar rishin yi wa yara rajista ne saboda rashin wayar da kan mutanen jihar.

” Duk da cewa muna gudanar da aiyukkan mu a jihar amma da dama basu da masaniya game da irin aiyukkan da muke yi.

” Idan ka matsa ka tambayi mutum game da aiyukkan mu sai kaji yace ai kirga mutane kawai muke yi amma basu da masaniya game da rajistan yara da mutuwa da muke yi.

Adamu yayi kira da a karo kafa rumfunar yi wa yara rijistan haihuwa domin a iya sanin yawan yaran da ake haihuwa domin tsara ayyukan ci gaba a jihar.

Share.

game da Author