2019: Masu son kan su da ragwaye daga cikin mu ne suka fice daga APC – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa dukkan wadanda suka fice daga APC zuwa sauran jam’iyyu mutane ne masu son kan su da kuma ragwaye, wadanda ba za su iya tafiya a bisa turbar muradin da wannan gwamnati mai ci a yanzu ta sa gaba.

Buhari ya yi wannan jawabi yayin da ya ke karbar fom din neman tsayawa takarar shugabancin kasar nan a aben 2019, a karkashin jam’iyyar APC.

Cikin watan Yuli wasu gwamnoni tare da Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki suka canja sheka da daga APC.

Akwai kuma gungun sanatoci da ‘yan majalisar tarayya da suka fice daga jam’iyyar mai mulki a wancan lokacin.

Wata kungiya ce mai suna Nigerian Consolidation Ambassadors Network (NCAN) ta sai wa Buhari fom din.

Buhari and NCAN

Buhari and NCAN

Buhari ya kara nanata cewa a yanzu cin hanci da rashawar da aka fara murna an kusa korar sa, to ya juyo a guje ya na yakar kasar nan.

“Amma yanzu mu na da jam’iyya mai cike da nagartattun mutanen da ke da muradin yi wa al’umma aiki tukuru, domin tabbatar da samun kasaitacciyar Najieriya.”

Buhari ya nuna godiyar sa ga kungiyar da ta sai masa fam wadda kungiya ce ta matasan kasar nan daga ko’ina da ta hada naira miliyan 50 kudin fam.

Buharin ya tuna da cewa muradin sa na ceto Najeriya ya fara ne tun daga 2002.

Ya ce Najeriya ta kusa fadawa ramin da ba ta iya fitowa cikin shekarar 2006, inda wasu mutane masu mummunar manufa suka wulakantar da zaben 2007.

Daga nan sai ya fara lissafa ayyukan da ya samu nasarar gudanarwa da suka hada da aikinn titin jiragen kasa, tallafin inganta noma, farfado da masana’antun takin zamani, Asusun Baidaya, wanda ya ce ya rage satar kudade da kuma samar da aikin yi a kasa da sauran su.

Buhari and Adamu Aliyu

Buhari and Adamu Aliyu

Share.

game da Author