Hanyoyi 5 da iyaye za su maida hankali a kai don ingata lafiyar jariran su

0

Mutuwar yara musamman ‘yan kasa da shekara biyar matsala ce dake matukar ci wa gwamnatin Najeriya tuwo a kwarya.

Bisa ga binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta gudanar ya nuna cewa mutuwar yara da jarirai ya karu daga yara 87 cikin 1000 dake mutuwa a shekarar 1990 zuwa 100 daga cikin 1000 a shekarar 2003.

” Binciken ya kara nuna cewa a Najeriya duk shekara jarirai 31 daga cikin 1000 na mutuwa,wadanda ke shan nono 70 daga cikin 1000 na mutuwa sannan ‘yan kasa da shekaru biyar 120 daga cikin 1000 ke mutuwa.

WHO ta ce an sami wannan sakamakon duk da yawan asibitoci da yiwa yara allurar rigakafi da ake yi a kasar.

Bayanai sun nuna cewa yawan mace macen yara kanana da Najeriya ke fama da shi na da nasaba ne da rashin zuwa asibitoci da mutanen kasar ke kin yi. Sannan idan har akwai babu tabbacin inganci a kulan da za a samu a asibitin.

” Bincike ya nuna cewa a shekarar 2003 mata biyu bisa uku ne suka haihu a gida sannan daya bisa uku ne ke haihuwa tare da taimakon kwararren ma’aikacin kiwon lafiya a Najeriya.

A dalilin haka ne wani likitan yara dake aiki a asibitin ‘Adeoyo Hospital’ dake Ibadan a jihar Oyo, Adesoji Abiona ya bayyana wasu hanyoyi da uwaye za su iya bi domin inganta kiwon lafiyar ‘ya’yan su.

1. Shayar da Jariri nonon uwa

Shayarwa hanya ce na ciyar da jariri abincin da zai rayar da shi ta hanyar bashi nonon uwa.

Mafi yawan lokuta al’adu da canfe-canfe su kan hana mata da dama shayar da jariran su nonon uwa.

Bayanai sun kuma nuna cewa idan mace ta shayar da danta zalla nonon uwa na tsawon watanni shida ko kuma shekara daya yana inganta kiwon lafiyar dan da kuma nata sannan hakan wata dabara ce na bada tazaran iyali.

2. Cin Abinci

Yayin da ake rainon yaro akwai lokacin da uwa zata fara ba danta abinci dik da tana bashi nono.

Abiona ya ce kamata yayi a tanaji kayan abinci masu bunkasa karfin garkuwan jiki kafin a fara ciyar da yaro.

Wadannan kayan abinci sun hada da manja, wake, kwai, kifi kayan itatuwa da sauran su.

Ya ce wadannan kayan abincin za su taimaka wajen kara kaicin kwakwalwar yaro tare da lafiyar sa.

Sannan itama uwa kamata yayi ta na cin abinci irin haka domin shima yaron ya dunga samu a ruwan nono yana sha.

3. Tsaftace muhalli da jiki

Domin bunkasa kiwon lafiyar ‘ya’ya kamata ya yi a tabbatar suna zaune a muhalli tsaftacacce da jikkunan su.

Abiona yace hakan na taimaka wa wajen hana yara kamuwa da cututtuka kamar su zazzabin cizon sauro, kwalara, ciwon ciki da sauran su.

4. Rigakafi.

Yin allurar rigakafi wa yara hanya ce na kare su daga kamuwa da cututtukan dake oya yi wa rayuwar su barazana.

Wadannan cututtuka sun hada da shan inna, bakondauro,shawara, zazzabin cizon sauro da sauran su.

5. Ganin likita.

Abionu yace ganin likita lokaci lokaci na da matukar mahimmanci domin haka na kiyaye yin abobuwan da ka iya cutar da kiwon lafiyar su.

Idan mace na zuwa ganin likita a lokutan da ya kamata likitan zai bata shawarwarin ababen da ya kamata ta yi da wadanda bai kamata ta yi ba sannan da yadda ita kanta za ta ringa kula da kanta.

Share.

game da Author