Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya na kulle-kullen hargitsin da zai rikita jihar sa domin ta yi nasara ko da karfin tsiya a zaben 2019.
Cikin wata tattaunawa da ya yi da wakilin PREMIUM TIMES a Fatakwal, babban birnin jihar, Wike ya ce akwai kulle-kullen da gwamnatin tarayya ke yi domin a kashe su don kawai a ci zaben jihar Rivers na 2019 ko da arziki ko da tsiya.
Ya ci gaba da cewa tuni ma har ya shaida wa iyalan sa cewa to zaben 2019 na jihar Rivers shi dai bakin rai bakin fama zai fito a fafata.
Wike ya ce gwamnatin tarayya ta fara nuna irin yadda na ta salon magudin ya ke tun a zaben jihar Ekiti inda ya yi ikirarin cewa an tafka magudi.
Da aka tambaye shi cewa abokin sa gwamna Ayo Fayose ya yi lakwas tun bayan da aka kayar da shi, sai Wike ya ce ba lakwas Fayose ya yi ba, amma ya na can ya maida hankalin sa wajen tattara hujjojin da zai gabatar wa kotu dmin a tabbatar wa kotu irin rashin kunyar tafka magudin da gwamnatin Buhari, kuma gwamnatin APC ta yi a zaben gwamnan jihar Ekiti.
An tambaye shi cewa alamomi a fili su na nuna cewa gwaman Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ne ya ke mara wa baya domin zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Wike ya ce kwata-kwata ba haka abin ya ke ba. Ya kara yin nuni da cewa shi ya na da wani irin hali, wato ba ya yada aboki don ya canja sheka daga jam’iyar da suke ya koma wata. Daga nan sai ya fara lissafa su Tambuwal, Kwankwaso, Saraki da sauran su ya ce duk abokan sa ne, kuma ko lokacin da suka fice daga PDP suka koma APC, bai yada zumunci da su ba.
Wike ya ce shi ba ya goyon bayan kowa, domin ba shi ne kadai ko wakilan jihar Rivers ne kadai za su yi zabe ba. Ya ce idan ba a manta ba, dukkan masu takarar shugabancin kasar nan a karkashin PDP sun kai ziyasa jihar sa kamar yadda suke kai wa saukran jihohi, kuma ya karbi kowa hannu bib-biyu.
Wike ya ci gaba da cewa shi ya na ma ganin cewa ba za a yi zaben 2019 a jihar Rivers ba, domin gwamnati za ta turo jami’an tsaron ta su yi ta harbe-harbe. Daga nan sai a dage zaben sai wani lokaci.
“Idan aka sake sa wata ranar kuwa, to a ranar zaben za su turo tulin jami’an tsaro su yi abin da suka ga dama kawai.”
An kuma tambayi Wike shin me zai hana idan haka ne ya bada kai bori ya hau, APC ta yi nasara a jihar Rives din, domin a kauce wa zubar da jinni?
Sai ya ce ai ba za ta taba yiwuwa ya ba ‘yan tabare dama su kassara siyasar jihar Rivers ba.
Wike ya ce ai ya ji duk kulle-kullen da gwamnatin APC ke yi na kokarin tada husuma su kwace jihar Rivers. Ya ce wasu da suka canja sheka daga APC zuwa PDP ne su ka yi masa wannan kwarmaton. Wannan kuwa mafarki ne kawai su ke yi, domin ba zai taba yiwuwa ba. Inji Wike.
Discussion about this post