Wasu kwararrun masana ilimin kimiyya dake jami’ar ‘Queen Mary’ a Landan kasar Britaniya sun gano hanyar kawar da cututtukan dake kama zuciya ta hanyar hada magungunan rage cututtukan dake kama zuciya da wadanda ke hana kitse taruwa a zuciya.
Ajay Gupta ya bayyana haka a taron masana kimiyya da ya wakana a garin Munich dake kasar Jamus.
Gupta yace sun hada magungunan rage cututtukan dake kama zuciya da wadanda ke hana kitse taruwa a zuciya a jikin wasu mutane masu shekaru 60.
” Sakamakon da muka samu daga wannan bincike ya nuna cewa da wadannan mutane suka kai shekaru 75 zuwa 80 ba a same su sun kamu da su kamu da cutar da ke kama zuciya ko kuma wanda ke sanya shanyewar bangaren jiki.”
Discussion about this post