KOMAWAR SHEKARAU APC: Ba a ga wulkawar Salihu Takai ba

0

Wani abin da ya daure wa mutane kai shine ba a ga Salihu Takai a taron canza shekar Shekarau ba, wadda shine ake wa ganin dan gaban goshin sa sannan ba a ga shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi 40 cikin 44 na jihar.

Shi dai Takai ana yi masa sanin cewa shine za a fi gani a gaba-gaba a wannan harka amma sai dai kuma aka ga ko keyar sa ma ba a gani ba a wajen taron.

Tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau ya tabbatar da komawar sa Jam’iyyar APC yau a garin Kano.

Idan ba a manta tun a makon jiya ne Shekarau ya bayyana rashin jin dadin sa kan yadda hedikwatar jam’iyyar PDP ta karkata wajen fifita Sanata Rabiu Kwankwaso tun bayan dawowar sa jam’iyyar.

Shekarau ya koka cewa an rusa shugabannin jam’iyyar aka mika wa Kwankwaso akalar jagorancin jam’iyyar.

Ranar Alhamis shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomole da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje suka yi wa Shekarau zawarci da tayin ya dawo APC.

Cikin wadanda suka koma APC sun hada da wasu da ga cikin shugabannin da aka sauke da kuma wasu daga cikin wadanda suka rike mukamai a lokacin da Shekarau ya ke mulki a jihar Kano.

Share.

game da Author