Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Kungiyar cigaban matasan shiyyar Daura (DEYPM) ta bayyana cewa ta ware naira miliyan 70 domin kashe wa a kamfen din tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.
Shugaban Kungiyar Abdulkadir Lawal yace kungiyar ta hada wannan kudi ne ta hanyar karo-karo daga mambobin kungiyar.
Lawal ya bayyana haka ne da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Daura.
Ya kara da cewa kungiyar za ta kashe Naira miliyan 40 wajen yi wa Buhari Kamfen sannan kuma miliyan 30 wajen tallata gwamna Masari.
Discussion about this post