Falalu Bello ya zama sabon shugaban jam’iyyar PRP

0

Jam’iyyar PRP ta sanar da nada tsohon shugaban bankin Unity, Falau Bello a matsayin shugaban jam’iyyar.

Idan ba a manta ba shugaban jam’iyyar Balarabe Musa ya sanar da sauka daga shugabancin jam’iyyar cewa rashin lafiya da nauyin jiki za su hana shi gudanar da ayyukan jam’iyyar yadda ya kamata.

A taron jam’iyyar da akayi a Kaduna, an nada Balarabe Musa a matsayin shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar.

Sauran mambobin sun hada da Ango Abdullahi (Arewa Maso Yamma), Bashir Magashi (Arewa Maso Yamma), Lawan Batagarawa (Arewa Maso Yamma), Datti Malumfashi (Arewa Maso Yamma), Mustafa Bello (Arewa ta Tsakiya da and Setly Dadzie.

Sauran sun hada da Ibrahim Usman (Arewa Maso Gabas), Ali Mala (Arewa Maso Gabas), Philip Afanmuo (Kudu Maso Yamma), Segun Falope (Kudu Maso Yamma), Laoye Sanda (Kudu Maso Yamma), Odidi (Kudu Maso Kudu).

Share.

game da Author