Osinbajo bai fahimci ma’anar sauya fasalin kasa ba – Atiku

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ba daidai ba ne furucin da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya yi cewa, gyara fasalin Najeriya ba shi ne matsalar wannan kasar ba.

A cikin wata makala da PREMIUM TIMES TIMES ta buga, wadda ofishin yada labaran Atiku ya aiko, ya ce Osinbajo ya nuna rashin gamsuwa ko godiya ko kuma rashin fahimtar abin da gyara fasalin kasa ke nufi.

Ya ce abin mamaki ne matuka a ce mutum kamar Mataimakin Shugaban Kasa bai fahimci ko kuma ya kau da kai daga fahimtar cewa rashin sauya fasalin kasar nan shi ne ke kawo cikas wajen ci gaban kasar da kuma maida ta koma baya.

“Akwai takaici mutum kamar Osinbajo ya yi wa sauya fasalin kasa fahimtar cewa kamar sauya fasalin shiyyoyin kasar nan ne, wanda kuma ba haka abin ya ke ba.”

“Sauya fasalin kasa ba wai magana ce kan sake karkasa shiyyoyi ko jihohin Najeriya ba, ko kuma sake shata kan iyakokin jihohi, a’a. Abu ne da zai kara zaburar da gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da kowane ya zabura domin ya zauna da kafafun sa, ta yadda ma zai rika samar da ayyukan yi da dimbin jari ga al’umma.

Ya kara yin nuni da cewa zaman jiran kudade da wasu jihohi da kananan hukumomi ke yi, ne ke sa ba su iya tashi tsaye wajen iya rike kan su, sai sun jira. Wannan kuwa inji shi ya na kashe kaifin kishin tattalin abin da ake samu, kuma ya na hana inganta albarkatun wasu yankuna balle a maida su hanyoyin samun kudaden shiga.

Atiku ya ce sake fasalin kasa zai cire gorin da ake yi wa wasu yankunan da ake ganin cewa ci-ma-zaune ne, kuma zai kara kawo hadin kai a cikin kasa a tsakanin shiyyoyi, yankuna da jihohi da kuma al’umma bai-daya.

Share.

game da Author