An gano karin gawawwakin sojoji 17 da Boko Haram suka kashe a harin Barno

0

An gano wasu gawawwakin sojojin barikin Zari dake jihar Barno da Boko Haram suka far wa inda suka kashe sojoji da dama sannan suka waske da manya-manyan kayan yaki da motoci a karamar hukumar Mobbar, jihar Barno.

Rundunar soji da ke gudanar da binciken da nemo inda sauran sojojin suke ne suka gano wadannan gawawwaki.

Idan ba a manta ba aranar Alhamis din da ta gabata ne Boko Haram suka far wa wani sansanin Sojojin Najeriya dake Zari, jihar Barno.

Wannan hari dai ya yi munin gaske domin kuwa bayanan da ya iske mu sun nuna cewa Boko Haram sun Kashe sojojin Najeriya akalla 31 sannan 19 suka samu raunuka daban-daban a jikkunan su.

Su dai Boko Haram sun far wa wannan sansani ne suna sanye da kayan sojoji.

Majiyar mu da ba ya so a fadi sunan sa ya bayyana mana cewa, sai da akayi kusan awa daya ana batakashi tsakanin sojojin Najeriya da Boko Haram a wannan hari kafin Boko Haram suka ci galaban mu.

Boko Haram sun kawo wannan hari ne a motocin yaki 12 sannan wasu da yawa daga cikin su suna tafe a kasa da misalin karfe 4:30 na yammacin Alhamis.

Har zuwa safiyar Asabar ba a iya tantance ainihin ko sojoji nawa ne suka rasu a harin ba.

Sauran sojojin da aka ji wa ciwo an kai su asibitin sojoji dake Maiduguri.

Majiyar mu sun shaida mana cewa bayan barnan da Boko Haram suka yi wa sojojin, sun arce da motocin Yaki, makamai, motocin daukar mara lafiya, motar ruwa, manya-manyan bindigogi da wasu makamai.

Sai dai kuma har yanzu ba a san ko wani bangaren Boko Haram ne suka kai wannan hari ba. Ko bangaren Shekau ne ko na Albarnawi.

Da muka nemi ji ta bakin Kakakin rundunar sojin Najeriya, Texas Chukwu, gane da abin da ya faru, hakan ya ci tura domin bai amsa wayar da akayi masa ba.

Sai dai kuma Konel Onyema Nwachukwu dake can Maiduguri ya shaida mana cewa anyi wa Boko Haram luguden wuta a wani hari da aka kai musu da jiragen yakin saman Najeriya.

” Abin da na sani game da abinda ya faru shine, anyi wa Boko Haram luguden wuta daga sama. Wato jiragen yakin Najeriya suka fatattake su sannan sun kashe da dama daga cikin su.

” Amma yanzu bani da masaniya wai har akwai wasu sojojin Najeriya da aka kashe a wannan hare-hare.

Wani Janar din Soji ya bayyana mana cewa abinda ke faruwa da sojojin Najeriya a filin daga abin tashin hankali ne matuka. An bari ana ta kashe su, saboda, son kai da rashin iya aiki, da munaficcin manyan sojojin dake shugabantar dakarun.

Ya ce a gaskiya gwamnatin Buhari ta gaza kwarai wajen yaki da Boko Haram.

” Maimakon a bari a na fada wa mutane gaskiya kan abin ke faruwa, sai ana bobboyewa sannan ana yi wa sojoji barazanar hukunta su da laka musu yi wa aikin soji bore.

Share.

game da Author