Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta ce karya ne, babu wanda ya kai hari a gidan Sanata Godswill Akpabio, kamar yadda kakakin yada labaran sa ya bayyana wa duniya.
Tun da farko dai kakakin yada labaran Akpabio ne, Anietie Ekong, ya bayyana cewa mahara sun bude wuta gidan sanatan da ke garin su na Ukana Ikot Ntuen, da ke jihar, da misalin karfe 7:30 na yammacin Talata.
” Wannan magana karya ce,” inji kakakin yada labaran ‘yan sandan jihar, Odiko MacDon, kamar yadda ya yi wa PREMIUM TIMES bayani a safiyar yau Laraba.
“ Abin da kawai ke akwai, shi ne, an yi yunkurin yin wani cashi da makami, a wani gidan mai da ke kusa da Gidan Sanata Akpabio, da ke da tazarar mita 200 da gidan sa.
“ Amma ba wanda ya kai wa gidan Sanata Akpabio din hari.” Haka Mataimakin Sufurtanda na ‘yan sanda ya bayyana wa Premium Times.
Shi ma DPO na Karamar Hukumar Essien Udim, ya tabbatar da cewa a wani gidan mai ne aka nemi yin fashi da makami, ba a gidan Akpabio ne aka kai harin ba.
“ Saboda ai akwai ma wasu ‘yan sanda a kusa gidan mai din, to lokacin da ‘yan fashin suka fara harbi, sai su na ‘yan sandan suka fara harbi, to sai ‘yan fashin suka arce.” Haka DPO din ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta sake tuntubar kakakin Sanata Akpabio wanda ya ce an masa hari har gida, ya shaida masa matsayar rundunar ‘yan sandan jihar, sai ya ce, “Abin da mu dai muka sani, shi ne an yi harbe-harbe a kofar gida, kuma bakin gate din gidan Akpabio.”
Karanta nan: An yi ruwan alburusai a gidan Akpabio