Kungiyar Miyetti Allah ta Kasa, ta nesanta kan ta daga wata barazana da kodinatan ta na jihar Benuwai ya yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.
A cikin wata tattaunawa da jaridar PUNCH, Garus Gololo ya gargadi Saraki ko dai ya sauka ko kuma a sauke shi da karfin tsiya.
Sai dai kuma a cikin raddin da Miyetti Allah ta Kasa baki daya ta maida wa Gololo, ta ce ba da yawun bakin ta ya yi wannan abin da su ka kira kasassaba.
A cikin wata takarda da kungiyar ta fitar, Sakataren ta ka kasa bakiya, Usman Ngelzarma, a yau Laraba ya ce kalaman Gololo na bakin sa ne shi kadai kawai.
Ngelzarma ya tabbatar wa PREMIUM TIMES wannan matsaya ta su da bakin sa.
Ya ce a matsayin Gololo na kodinatan jihar Benuwai, ba shi da wani hurumi ko umarnin da zai yi magana da yawun kungiyar Miyetti Allah ta kasa baki daya.
Daga nan ya kara da cewa babu ruwan kungiyar su da shiga sha’anin siyasa ko rikicin siysa ballantana har ta goyi bayan wani bangare.
Discussion about this post