Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya maida wa jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu martanin cewa ya na da duk abin da ake bukata don tsayawa takarar shugabancin Najeriya da Muhammadu Buhari a 2019.
Tambuwal ya yi wannan kalami ne a matsayin martanin sa ga Bola Tinubu, wanda ya ce Tambuwal ya fice daga APC ne saboda ya makance da neman zama shugaban kasa, wanda kuma ginar sa ba cimma ruwa za ta yi ba.
Sai dai kuma a shafin tiwita na Gidan Gwamnatin Jihar Sokoto, Tambuwal ya musanta zargin da Tinubu ya yi masa inda ya ce “Idan da ina neman zama shugaban kasa ne, ai da a cikin APC zan zauna na buga takara tare da Shugaba Buhari. Saboda ina da duk abin da ake nema na tsayawa takara da Buhari.
“Tinubu ya yi kokarin zama uwa-makarbiyar komai a kasar nan, a lokacin da aka hana shi kujerar mataimakin shugabancin kasar nan. Shi a na sa tunanin, kowa ma ya rika yin irin dabi’un sa. Idan naga dama ai da na tsaya cikin APC na buga takara da Buhari. Kuma kuri’a ce kawai za ta tantance wanda zai yi nasara.
“Wato Tinubu na nuna babu adalci a cikin APC, babu bin tafarkin dimokradiya kenan, kuma jam’iyya ce mai tauye wa wasu ‘yancin su na neman tsayawa neman wani matsayi da dimokradiyya ta halasta musu?
“Ai tuni na rigaya na bayyana dalilai na na ficewa daga APC, kuma wadannan dalilai duk su na nan, batun takara kuma ba ya ma ciki.” Inji Tambuwal
Idan ba a manta ba Jagoran Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya zayyano wasu dalilai da ya sa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal suka fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
A wata takarda da ya saka wa hannu da kan sa Tinubu ya ce babban dalilin da ya sa Saraki da Tambuwal suka fice daga APC shine don su cimma burin su na siyasa da ke kokarin fin karfin su muddun za su ci gaba da zama a jam’iyyar APC.
” Sauran ‘yan siyasar kuma duk sun koma PDP ne domin basu samun abin da suke nema ba wato a raba kudaden jama’a su handame su.
” Shi Tambuwal buri ce ta cika shi fam. So yake ya nemi takarar shugabancin Najeriya. Amma kuma Buhari yayi masa katangar karfe tsakanin sa da wannan kujera. Shi ne ya lallaba ya tattauna da gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike, inda ya yi masa alkawarin za a bashi tikitin takara a PDP idan ya sauya sheka.
” Bayan haka kuma wani abu da ya kara tada masa da hankali shi ne alamu da ya gani cewa kujerar gwamna ma da ya ke kai sai ya yi takarar fidda gwani da sauran ‘yan takara a APC.
” Idan ba don gwamna Wike ya yi masa alkawarin zama dan takarar PDP ba ina ganin da bai fice daga APC ba.” Inji Tinubu
” Shi ko Saraki ta sa tayi kama da ta Tambuwal domin shima shugabancin Najeriya yake so, amma Buhari yayi masa Katangar karfe.
Idan har yace zai fito takara to zasu gwabza da su Tambuwal kenan. Sai dai ya shinshino hakan, sai yake neman goyon bayan yan PDP din da ko ta halin kaka ya iya dawowa majalisa a matsayin shugaban ta.
Tinubu ya ce sauran ‘yan siyasan da suka fice kuwa duk kwashi kwaraf ne masu neman ko ta halin kaka a raba kudin kasa maimakon ayi wa mutane aiki da su.
Shi ko Tambuwal ya bayyana cewa wannan duk ra’ayi ne na Tinubu domin shi ba haka ne dalilan sa na barin jam’iyyar APC ba.