A akalla mutane 11 sun rasa rayukan su a wani hadarin mota da aka yi a hanyar Maje dake karamar hukumar Suleja a jihar Neja.
Shugaban hukumar FRSC Yusuf Garba ya sanar da haka ranar Alhamis da yake zantawa da wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Minna.
Garba ya bayyana cewa hadarin ya auku ne da karfe 5:30 na safiyar Alhamis. Sannan a kalla mutane 11 ne suka rasu, 14 kuma suka sami raunuka daban daban.
” A yanzu dai mutane 14 din da suka sami rauni an kwantar da su a babbar asibitin Sabon Wuse.”