Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) na yin juyayin rasuwar daya daga cikin ma’aikacin ta mai suna John Iliya da ya rasu a wajen aiki sanadiyyar hari da Boko Haram suka kai wa wasu sojojin Najeriya da yake aiki tare da su.
Shugaban hukumar NEMA, Mustapha Maihaja ya sanar da haka da yake ganawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce Boko Haram sun kashe Iliya ranar Laraba 8 ga watan Yuli a Damasak, jihar Barno.
Maihaja, ya kara da cewa bayan Iliya da suka rasa, hare-haren Boko Haram yayi sanadiyyar mutane sama da miliya 2 da su rasa matsugunin su a jihar.
” Bayan haka ire-iren wadannan hare-hare bai tsaya a kasa Najeriya ba kawai, ya tsallaka har zuwa kasashen Chadi da Kamaru.
A karshe Maihaja ya ce za a dawo da gawar Iliya gida domin iyalen sa su binne shi.
Discussion about this post