Majalisa za ta amince da kasafin kudaden zaben 2019 cikin mako mai zuwa – INEC

0

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa nan da mako daya mai zuwa Majalisar Dattawa za ta rattaba hannun amimcewa da kasafin kudaden da za a kashe a lokacin zaben 2019 na naira bilyan 242.

Yakubu ya yi wannan bayani ne bayan wata ganawa da ya yi da manema labarai a jiya Laraba, a Majalisar Tarayya.

Ya kara da cewa an yi wa hukumar ta sa tabbacin cewa Majalisar Tarayya za ta yi matukar kokarin ganin an amince da batun, domin ita ma ta na da muradin ganin abin da aka sa gaba na gudanar da zabe ya gudana cikin nasara.

Ya ce Majalisa ta gayyaci INEC ce domin ta yi bayanin muhimmanci da kuma makasudinn yadda za a kashe kudaden a lokacin zabe na 2019.

“Daga yau saura kwanaki 191 a bude rumfunan zabe da karfe 8 na safe daidai, a ranar 16 Ga Fabrairu, 2019.

“Kun ga kenan akwai wasu aikace-aikace da za a rika gudanarwa a cikin wadannan tsawon lokaci zuwa ranar zabe.

“Yadda kawai za a iya samun wannan nasara shi ne ya kasancwe ka na da dukkan kayayyakin da ake bukata domin zaben ya samu inganci.

“ Babu yadda za a yi ka iyi aiki sosai sai idan ka na da kayan aiki.”

Share.

game da Author