Babu ranar dawowar Majalisar Tarayya – Saraki, Dogara

0

Majalisar Tarayya ta bayyana cewa ba ta sa ranar dawowa zaman duba amincewa da kasafin kudin da INEC za ta kashe a wurin gudanar da zaben 2019 ba.

Shugabannin Majalisar, Bukola Saraki da Yakubu Dogara ne suka bayyana haka a cikin wata takardar hadin-guiwa da kakakin yada labaran su, Yusuf Olanionu da Turaki Hassan suka sa wa hannu.

Ana sa ran majalisar za ta yi zaman hadin-guiwa ne, bayan da aka tabbatar da yiwuwar haka, bayan wani zama da aka yi tare da shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu, kafin ta tafi hutu.

Daga cikin abin da aka yi niyyar tattaunawa idan an zauna, har da batun amincewa da naira biliyan 242 da INEC ta rattaba cewa za ta kashe a wajen gudanar da zaben 2019.

Wasu ‘yan majalisar tarayya sun bayyana wa PREMIUM TIMES tun a ranar Litinin cewa ba a kira su cewa su koma majalisar ba.

Cikin takardar hadin-guiwa da Saraki da Dogara suka fitar a yau Talata, sun ce har yanzu ba a saka wata ranar dawowa ba, a bisa dalilin cewa baya ga batun kasafin kudin INEC, akwai wasu batutuwan da za a tattauna idan an dawo, kuma har yanzu su na hannun kwamitocin da ke duba su, ba a ma fara dubawa ba tukunna.

Sun ce akwai aikin duba batun bukatun na INEC da ke a hannun kwamitocin INEC na Majalisar Dattawa da ta Tarayya, wadanda dama da su ne INEC din za ta zauna, to kuma har yanzu kwamitocin ba su yi zaman nazarin bukatun ba.

Akwai kuma rahoton Majalisun biyu kan Kasafin Kudade, Lamuni da Basussuka na tsabar kudin Euro, wadanda idan an dawo su ma za a duba su, to amma har yau ba a zauna ba tukunna.

Sun ce idan kwamitocin nan ba su kammala aiki ba, babu yadda za a yi a dawo majalisa, musamman ga shi an bada hutun ne dama domin wasu su samu damar tafiya aikin Hajji.

Saraki da Dogara sun ce dalili kenan ma aka sa ranar dawowa majalisa a ranar 25 Ga Satumba, 2018.

Share.

game da Author